Connect with us

Addini

Rahoto: Haɗuwar Arfa da Juma’a rana ɗaya daraja ce ga musulmai – Limamin Tukuntawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na masjidul kuba da ke unguwar Tukuntawa, malam Ahmad Ali ya ce, haduwar Arfa da juma’a rana daya ba karamar lada ce ga al’ummar musulmi ba.

Malam Ahmad Ali, ya bayyana hakan ne, yayin da yake Karin bayani dangane da abinda hudubarsa ta kunsa.

Wakilin mu na Ibrahim Abdullahi Soron Dinki yana da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Addini

Hajji2025: Maniyyatan Najeriya 16,182, sun sauka a Saudiyya – NAHCON

Published

on

Hukumar kula da Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta ce izuwa yanzu aƙalla maniyyatan ƙasar su 16,182, ne suka sauka a ƙasar Saudiyya, domin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2025.

Hukumar ta NAHCON, ta bayyana hakan ne da yammacin Alhamis ɗin nan a shafinta na Facebook, ta ce aƙalla jirage 40, ne suka yi jigilar maniyyatan, daga ranar juma’ar da ta gabata, da aka fara kai maniyyatan zuwa ƙasa mai tsarki.

 

NAHCON, ta ƙara da cewa, jirgi na ƙarshe da ya sauka a Madinah, shi ne jirgin UMZA, mai lamba UMZ3412, da ya tashi ɗauke da maniyyatan jihar Kaduna su 299, Maza 229, mata kuma 70, sai wasu na musamman su 9.

Continue Reading

Addini

Hajjin2025: Maniyyatan Najeriya 3,644, sun sauka a Saudiyya

Published

on

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta ce zuwa yanzu Maniyyatan ƙasar nan su dubu 3,644, ne suka sauka a ƙasa mai tsarki, domin sauke Farali a aikin hajjin bana, na shekarar 2025.

Kazalika, hukumar ta ce aƙalla jirage Tara ne suka yi jigilar maniyyatan, biyo bayan saukar maniyyatan jihar Oyo su 550, Maza 302, Mata kuma 248, wanda jirgin ya sauka da misalin ƙarfe 05:54 na yammacin yau Asabar.

A ranar Juma’a 09 ga watan Mayun 2025, ne dai mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shateema, da shugaban hukumar Alhazai na ƙasa NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale Usman, da gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma, suka ƙaddamar da tashin Maniyyatan a birnin Owerri na jihar Imo.

Continue Reading

Addini

Harsuna 20 da za’a fassara huɗubar Arfah ta 2025, ciki har da Hausa a Saudiyya.

Published

on

Hukumar kula da aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya, ta ce za’a fassara huɗubar Arfah, ta shekarar 2025/1446, zuwa harsuna guda 20.

Shafin sada zumunta na Inside the Haramain Sharifai, ne ya wallafa hakan, yana mai cewa harsunan da za a fassara huɗubar ta Arfah, sune kamar haka.

1. Turanci
2. Faransanci
3. Malay
4. Urdu
5. Farisa/Farsi
6. Sinanci
7. Turkanci
8. Rashanci
9. Hausa
10. Bengali.

Sauran harsunan sune kamar haka.

11. Harshen mutanen Sweden
12. Harshen mutanen Espanya
13. Swahili
14. Amharic
15. Italiyanci
16. Fotigal
17. Bosniya
18. Malayalam
19. Harshen Filifino
20. Jamusanci.

Continue Reading

Trending