Connect with us

Addini

Rahoto: Cin haramun na hana Allah Ya amsa addu’a – Limamin Tukuntawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa, a jihar Kano, malam Ibrahim Abubakar Tofa, ya ce, cin haramun na hana Allah Ya amsa addu’ar mutane.

Malam Abubakar Tofa, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Akwai cikakken bayanin hudubar a muryar da ke kasa.

Audio Player

Addini

Harsuna 20 da za’a fassara huɗubar Arfah ta 2025, ciki har da Hausa a Saudiyya.

Published

on

Hukumar kula da aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya, ta ce za’a fassara huɗubar Arfah, ta shekarar 2025/1446, zuwa harsuna guda 20.

Shafin sada zumunta na Inside the Haramain Sharifai, ne ya wallafa hakan, yana mai cewa harsunan da za a fassara huɗubar ta Arfah, sune kamar haka.

1. Turanci
2. Faransanci
3. Malay
4. Urdu
5. Farisa/Farsi
6. Sinanci
7. Turkanci
8. Rashanci
9. Hausa
10. Bengali.

Sauran harsunan sune kamar haka.

11. Harshen mutanen Sweden
12. Harshen mutanen Espanya
13. Swahili
14. Amharic
15. Italiyanci
16. Fotigal
17. Bosniya
18. Malayalam
19. Harshen Filifino
20. Jamusanci.

Continue Reading

Addini

Hukumar Shari’a ta shirya buɗe baki ga Mutanen da suka musulunta a Kano

Published

on

A ƙoƙarin ta na ƙara ɗaɓɓaƙa harkokin addinin Musulunci, hukumar Shari’ah ta jihar Kano da haɗin guiwar kungiyar World Assembly of Muslim Youth (Wamy), sun shirya wa waɗanda suka karbi addinin Musulunci shan ruwa a ranar Lahadi 23 ga Ramadan shekarar 1446.

Taron shan ruwan dai ya gudana ne a harabar hukumar karkashin Jagorancin Mukaddashin Shugaban ta Sheikh Ali Ɗan Abba.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Muƙaddashin Daraktan yaɗa labarai na hukumar shari’a ta jihar Kano, Musa A Ibrahim (Best Seller).

Hukumar Shari’ar ta kuma ayyana ranar 15 ga Ramadan domin ta zama ranar da za ta rinƙa shan ruwa da waɗanda suka karɓi addinin Musulunci da za a rinƙa yi a duk shekara.

“Muna kuma miƙa godiya ga gwamnatin jihar Kano a karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf, da ƙungiyar World Assembly of Muslim Youth [WAMY] da suka ba mu gudummawa wajen shirya wannan taron, “in ji Sheikh Ali”.

Taron shan ruwan dai ya sami halartar dukkanin shugabannin hukumar da mambobin ta da kuma ma’aikatanta tare da shugabannin kungiyar WAMY, da wasu manyan mutane da suka halarta.

Da yake nasa jawabin wakilin shugaban kungiyar Wamy Alhaji Sanusi, ya nuna jin daɗinsa da yadda wannan shan ruwa ya gudana, kuma ya tabbatar da cewar kungiyar su ƙungiya ce ta taimakon addinin musulunci da musulmi a ko ina suke, kuma kungiyar zata ci gaba da wannan aikin alherin da izinin Allah S.W.T.

Continue Reading

Addini

Ku taimakawa mabuƙata da Naman Sallah bisa halin matsin rayuwar da ake ciki – Limami

Published

on

Babban limamin masallacin juma’a na Alaramma Abubakar Ɗan Tsakuwa, da ke unguwar Ja’en Ring road Mallam Abdulkareem Aliyu, ya yi kira ga al’ummar Musulmi, da su kiyaye ƙa’idojin yanka Dabbobin Layyah, domin gujewa cin mushen Nama.

Mallam Abdulkareem Aliyu, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u, lokacin da yake tsokacin huɗubar da ya gabatar ranar Sallar Idin da ya jagoranta a masallacin ranar Lahadi 17 ga watan Yunin 2024.

Ya ce a mafi yawan lokuta al’umma sukan yanka dabbobi amma rashin bin ƙa’idojin yanka yakan sanya wa su ci mushen nama ba tare da sun sani ba, a dan haka su tashi tsaye wajen sanin yadda ake yanka Dabbobin a mahanga ta addinin Musulunci.

A cewar sa, “Musulmai ku kwaɗaitu da yin sadakar naman layya musamman ma ga masu ƙaramin ƙarfi domin rabauta da rahamar Ubangiji S.W.T, “in ji shi”.

Mallam Abdulkareem Aliyu, ya kuma ce, akwai buƙatar a kiyaye nau’ikan dabbobin da aka sahale ayi layya da su, waɗanda suka haɗar da nau’in Sa ko Saniya, da kuma Raƙumi ko Raƙuma (Taguwar), ko kuma Rago ko Tinkiya, ko Akuya ko kuma Ɗan Akuya.

Wannan dai na zuwa ne bayan da al’ummar Musulmin Duniya suka gudanar da babbar Sallah, a jiya Lahadi 16 ga watan Yunin shekarar 2024.

Continue Reading

Trending