Connect with us

Manyan Labarai

Mafaruta sun gano wasu katunan zabe 320 da a ka boye su a cikin jaka

Published

on

Kungiyar Mafaruta sun gano wasu katunan zabe na dindindin guda 320, da aka boye su a wani kango a kan titin Ogbia a jihar Bayelsa.

Jami’an mafarauta da tsaron gandun daji na kasa ne suka gano su, inda suka jibge a cikin jaka, a lokacin da suke sintiri a yankin a ranar Talata.

Kwamandan mafarauta da tsaron dazuka na jihar, Moses Okano, wanda ya bayyana hakan a garin Yenagoa, yayin da yake mikawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun tsere a lokacin.

“Don haka, mun sami damar shiga ginin kuma abin da muka gani shi ne katunan zabe da aka yi watsi da su. Don haka, da sanin cewa wadannan kayan mallakar Gwamnatin Tarayya ne, kuma hukumar da doka ta ba su ko kuma ta ba su ikon rike wadannan abubuwa, ita ce INEC, don haka ya zama dole mu kwato su, muka yanke shawarar kawo su ga hukumar.”

Da yake karbar katinuna zaben a madadin kwamishinan zabe na jihar Bayelsa, sakataren gudanarwa na hukumar, Okop Umo-Obong, ya yabawa hukumar mafarauta da dazuzzukan da ta kawo wa hukumar katunan tare da kiyaye zaman lafiya a unguwar.

Manyan Labarai

Da na hadu da kwankwaso da sai na mare shi – Ganduje

Published

on

Tsohon Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace da sun hadu da kwankwaso da akwai yiyuwar ya mare shi, a fadar shugaban kasa.

Tsohon Gwamnan ya bayyana Hakan ne yayin wata ganawa da gidan television na channels, yayin da yake martani Kan ganawar shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu da Kuma jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a yammacin wannan juma’a.

” Nasan yana gidan Amma bamu hadu ba, da mun hadu akwai yiyuwar na kwada masa Mari” inji Ganduje.

Idan za’a iya tunawa dai kwanakin baya shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu yayi wata ganawa da kwankwaso, lamarin da aka jiyo tsohon Gwamnan na korafi cewa ba’a Yi musu adalchi ba, Koda dai a wancan lokaci, Ganduje ya musanta, ta bakin tsohon kwamishinan yada labarai Muhammad Garba, inda yace ba muryar Ganduje bace.

Wannan dai na zuwa ne a Gabar da gwamnatin Kano ke cigaba da rushe wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje ta cefanar ba bisa ka’ida ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gargadin Gwamnatin Kano Kan masu kaya a wuraren gwamnati

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi dukkanin masu kaya a wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta cefanar ba bisa ka’ida ba, dasu kwashe kayan su cikin gaggawa.

Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Dakta Abdullahi Baffa Bichi ta fitar ta bayyana cewa, dukkanin masu kaya a shagunan da aka gina a jiki ko cikin makarantu, Maƙabartu, Asibitoci, Masallatai, gefen badala, Filayen ma’aikatu, Filayen wasanni da sauran wuraren shakatawa mallakin gwamnati da cewa suyi gaggawar kwashe dukkanin kayan su dake cikin shagunan da aka gina a waƴannan gurare ba tare da ɓata lokaci ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Abba Gida Gida ya fara rusau

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta fara rushe wasu gine gine da aka yi su a wuraren gwamnati Ba bisa ka’ida ba.

A cikin daren Asabar din nan ne tawagar Kwamitin kar ta kwana mai lura da rushe gine gine ta fara da rushe wani sabon rukunin shaguna mai kunshe da sama da shaguna 90 dake jikin filin sukuwa a jihar Kano.

Mai magana da yawun gwamnan Kano Sunusi Ahmad Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewar wannan aiki somin tabi ne domin batun rushe gine ginen da aka yi su akan filayen jama ar Kano lamari ne da babu gudu babu ja da baya kamar yadda gwamna Engr Abba Kabir Yusif ya bayyana a lokacin da yake yakin neman zabe.

Tawagar kwamitin na kar ta kwana zai cigaba da rushe dukkan wasu gine gine da aka yi su ba bisa kaida ba.

Continue Reading

Trending