Connect with us

Labarai

Da Duminsa: An bayar da belin Ahmed Idris dakataccen Akanta na kasa

Published

on

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta bayar da belin dakataccen babban Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris da sauran wadanda a ke tuhuma bisa sharuddan da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta bayar.

Da ya ke yanke hukuncin, mai shari’a, Adeyemi Ajayi, ya ba da umarnin cewa, wadanda a ke tuhumar ba za su bar birnin tarayya ba, kuma idan sun so sai su nemi izinin kotu ko kuma a soke belinsu.

Kotun ta kuma bayyana cewa, wadanda ake tuhumar za su rattaba hannu kan yarjejeniyar cewa, za su bi sharuddan belin da EFCC ta gindaya.

Mai shari’a Ajayi, ya kuma ba da umarnin cewa, wadanda a ke tuhumar ba inda za su je har sai an kammala shari’ar, bayan sun ajiye fasfo dinsu na asali ga hukumar.

Alkalin kotun ya bayar da hukuncin ne bisa hujjar cewa, har yanzu ba a tabbatar da zargin da ake yi wa wadanda ake tuhumar ba.

Kotun ta kuma bayyana cewa, bisa tsarin doka, wadanda a ke tuhumar suna da damar bayar da belinsu, duk da zargin da a ke yi musu, tun da mai gabatar da kara bai bayyana cewa, wadanda a ke tuhumar sun aikata ba daidai ba a lokacin da suke hannun EFCC.

An fara shari’a kai tsaye bayan yanke hukuncin neman beli. A cewar The Cable.

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Trending