Connect with us

Labarai

Da Duminsa: Kotu ta bayar da izini a rataye mutanen da suka kashe Hanifa har sai sun daina motsi

Published

on

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 5 karkashin jagorancin mai shari’a, Usman Na’abba, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutane biyu wadanda kotun ta same su da laifin hada baki garkuwa da neman kudin fansa da kuma kisan kai.

Wadanda a ka samu da laifin sun hadar da: Abdulmalik Tanko da abokinsa Hashim Isyaku wadanda a ka samu da laifin kashe yarinya yar shekaru 6 mai suna Hanifa Abubakar, bayan sun yi garkuwa da ita.

Masu gabatar da kara sun kawo shaidu 8, yayin da wadanda a ke tuhumar suka kare kansu.

A yayin hukuncin wanda ya dauki kusan awanni uku a na yi, mai shari’a Na’abba, ya ayyana cewar, masu gabatar da kara sun tabbatar da laifin ta hanyar kawo shaidu, kuma babu kokwanto cewar, Abdulmalik Tanko da Hashim Isyaku sune su ka yi garkuwa da Hanifa, kuma suka kashe ta, domin haka ya ayyana cewar, suma a rataye su har sai sun daina motsi.

Mai Shari’a Na’abba, ya kuma bayyana cewar, shaidu sun gaza alakanta Fatima Musa da laifin kisan kai, sai dai ya same ta da laifin yunkurin taimakawa masu garkuwa da kuma yunkurin taimakawa a aikata laifi, domin haka kotun ta hore ta da daurin shekara daya kowanne laifi.

A laifin hada baki domin aikata laifi an daure Abdulmalik shekaru 5, yayin da abokinsa Hashim a ka daure shi shekaru 2.

Gwamnatin jiha ce dai ta gurfanar da mutanen uku, wadan da ake tuhuma da laifin hada baki garkuwa da mutum da kuma kisan kai da taimakawa a aikata laifi.

A ranar 4 ga watan Disambar 2021 ne dai a ka sace Hanifa yayin da a ka taso su daga makarantar Islamiyya.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending