Connect with us

Manyan Labarai

Zan goyi bayan yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki saboda ƴan ƙasa – Atiku

Published

on

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin cewa, zai goyi bayan kwaskwarima ga kundin tsarin mulki, domin daukaka darajar ƴan kasa idan ya samu dama a zaɓen 2023.

A cikin sanarwar da mai taimaka masa a kan harkokin yaɗa labarai, Abdulrasheed Shehu, ya sanya wa hannu tare da aike wa Dala FM, ya rawaito cewa, Atiku na wannan kalan ne a wani taro da matasan Jam’iyyar PDP a fadin ƙasa, su ka kaddamar da wani shiri mai taken PDP sabon karni, a dakin taro na Shehu Musa Yar’adua dake Abuja, domin wayar da kan yan Najeriya.

A cikin mahalarta taron harda shi kan sa dan takarar shugabancin kasa, Atiku Abubakar da mataimakin sa Sanata Ifeanyi Okowa, sai shugaban Jam’iyyar, Sanata Dr Iyorchia Ayu da Boni Haruna da Liyel Imoke, tsohon gwamnan Cross River da gwamnan jihar Taraba gami da tsofaffin sanatoci da yan majalisar wakilai masu ci da kuma sauran jiga-jigan Jam’iyyar PDP.

A jawabin sa, dan takarar shugaban kasar, ya godewa matasan bisa wannan yunkuri, inda ya bukaci da su zage dantse, domin gina cigaba da hadin kan kasa. Ya jaddada bukatar samun gwamnati wadda za ta tallafawa matasa da mata, domin basu damar aiki da basirar su ga aikin gina kasa.

Sanarwar ta kuma ce, kamar yadda ya fada a yayin gangamin yakin neman zaben gwamnan jihar Osun, ya bukaci matasan su karbi katunan zaben su, kuma su shirya yin zabe tare da kare kuri’ansu.

A nasa bangaren, shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, ya godewa matasan, bisa bujuro da wannan tsari, inda ya yi kira a garesu su yi aiki tare da Wazirin Adamawa wanda ya ce, ya sanya dukiyar sa ta kashin Kai a ilimantar da matasa a dukkan matakai, kuma yana cikin wadanda suka tsara managartan manufofi kan ilimi a can baya.

Babban mai jawabi a yayin taron, Emana Ambrose Amawhe Wanda Yar’ Takarar mataimakin gwamna ce a zaben badi, ta godewa tsohon mataimakin shugaban kasar kasancewar sa Mai farfado da kyakkyawan fata ga mutane, inda tace suna tare da Atiku Abubakar, saboda kyakkyawan kundin manufofin sa da kuma son sa ga tafiya tare da kowa domin zaman lafiya da fahimtar juna.

Wadanda suka shirya taron sun ce, sun kaddamar da kashin farko na tsarin a ranar 24 ga watan Afrilun bana, Inda suka ce wannan shi ne na biyu, kuma taken sa shi ne sake tsara Najeriya Wanda ke nufin sake hade kan jama’a, habaka tattalin arziki da ilimi da ingantaccen tsarin fedaraliyya . Kuma sun yi alkawarin wayar da kai da horar da yan Najeriya domin su fahimci nauyin dake kan su a matsayin su na yan kasa.

Manyan Labarai

Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Published

on

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.

Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a

“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.

Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.

Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.



Continue Reading

Manyan Labarai

An ga watan ƙaramar Sallah a Najeriya – Sarkin Musulmi

Published

on

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya, inda za a yi karamar Sallah gobe Lahadi.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a cikin daren Asabar ɗin nan, ya ce sun samu rahotannin ganin watan ne daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce daga cikin guraren da aiko musu da ganin jinjirin watan na Shawwal akwai Zazzau, da kuma daga Sarkin Dutse, da Arugungu, da kuma Shehun Borno, da dai sauran gurare daban-daban na Najeriya.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su gabatar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali, tare da taimaka wa mabuƙata.

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, biyo bayan sanarwar fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, ya kasance ranar Lahadi take 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446, wato ranar ƙaramar Sallah.



Continue Reading

Manyan Labarai

Shugaba Tinubu da Sifeton Ƴan Sanda ku bi wa mutanen mu da aka yi wa kisan gilla hakƙin su – Rt. Hon. Rurum

Published

on

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rabo, Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum, ya bayyana kaɗuwar sa bisa kisan gillan da aka yi wa wasu Mafarauta su kusan 16, a garin Uromi da ke jihar Edo, a lokacin da suke hanyar su ta komawa Kano daga jihar Rivers.

Honarable Kabiru Rurum, ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da aka aikowa Dala FM Kano a ranar Asabar, ya ce daga cikin mutanen da aka ƙona akwai mutum 11 da suka fito daga mazaɓun yankin sa na Kibiya da Bunkure, inda wasu 6 suka samu muggan raunuka suna karɓar Magani yanzu haka a jihar Edo.

A cewar Ɗan Majalisar, “Wannan abu da matasan garin Uromi a jihar Edo, suka yi ya saɓa da dokar kasa, kuma mummunan laifi ne, a don haka za mu bi kadin hakƙin mutanen mu da aka kashe a kuma waɗanda aka jikkata, “in ji shi“.

Kabiru Rurum, ya ce a matsayinsa na wakilin mutanen da aka kashe a majalisar Wakilai ta ƙasa, yana kira ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, da babban Sifeton ƴan sanda, da su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an kamo waɗanda suka yi wannan aika-aikar tare da hukunta su, da kuma biyan diyya ga iyalan waɗanda suka rasu da kula da waɗanda suka jikkata.

“Kasancewar wannan bashi ne na farko da ake samun wasu ɓata gari na tare matafiya akan hanya da basu ji ba basu gani ba su kashe su, a don haka muna fatan wannan karon gwamnati da sauran hukumomin tsaro za su ƙaddamar da ƙwaƙƙwaran bincike don ɗaukae mataki kamar yadda dokar kasa ta tanada, “in ji Rurum”.

Ɗan majalisar ya kuma jajantawa dukkanin al’ummar jihar Kano musamman Iyalan waɗanda suka rasu, tare da addu’ar Allah ya gafarta musu yasa Jannatul Firdausi makomar su, su kuma waɗanda suka jikkata Allah ya basu lafiya.



Continue Reading

Trending