Connect with us

Labarai

Rashin Tsaro: FRSC ta bayar da umarnin kama Baburan da ba su da rijista

Published

on

Shugaban hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa FRSC, Dauda Biu, ya umarci kwamandojin hukumar na sassan jihohi 37, da su kama duk wani Babur bai yi rajista da hukumar ba.

Biu ya ba da umarnin ne a wata sanarwa da jami’in wayar da jama’a na hukumar, Bisi Kazeem ya fitar a Abuja ranar Litinin. A cewar jaridar Guardian.

“Dukkan baburan da ba su da rajista za a kama su. A na bukatar masu baburan su kammala cikakken rajistar baburan kafin a sako su. Wannan zai bayar da hadin kai wajen masu aikata laifi da Babur “.

“Duk Baburan da aka kama, dole ne a rubuta cikakkun bayanai,’ in ji shi.

Shugaban na FRSC ya ce, umarnin ya zama dole ne, biyo bayan karuwar yawan Baburan da ke bin hanyoyi.

A cewarsa, akwai kuma bukatar a kama duk Baburan yadda ya kamata a cikin kundin tsarin tantance ababen hawa na kasa.

Ya yi nuni da cewa, umarnin zai taimaka wajen dakile rashin tsaro, idan duk Baburan da aka kama suna cikin ma’adanar bayanai ta kasa.

Biu ya bukaci kwamandojin sassan da su gaggauta tuntubar hukumomin tattara kudaden shiga na jihohinsu, domin kafa kwamitin da zai magance lamarin.

Ya kuma ba da umarnin cewa, a yi hadin gwiwa da jami’an ‘yan sanda da ofishin binciken ababan hawa da sauran masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da aiwatar da aikin.

Labarai

Rahoto: Mu nisanci abinda Allah Ya hana domin samun saukin rayuwa – Limamin Tukuntawa

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa a jihar Kano, Malam Ahmad Ali, ya ce, al’umma su duba tsakanin su da Allah tare da nisantar abinda ya hana, domin saukin tsadar rayuwa.

Malam Ahmad Ali, ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa wakilin mu na ‘yan Zazu,  Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, Karin bayani dangane da abinda hudubar da ya gabatar ta kunsa.

Akwai cikakken bayanin hudubar a muryar da ke kasa.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rubutu na da muhimmanci a mu’amalar bashi – Limamin Bompai

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke unguwar Bompai, SP Abdulkadir Haruna, ya ce, akwai bukatar mu rinka gudanar da mu’amalar bashi yadda addinin musulunci.

SP Abdulkadir Haruna, yana bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, bayar idar da Sallar Juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashi ya yi yunkurin cinye tabar Wiwin da aka kama shi da ita a hanyar kotu

Published

on

Ana zargin wani matashi ya yi yunkurin hadiye tabar Wiwi da miyagun kwayoyi da aka kama shi da ita a hanyar kotu.

Tunda fari jami’an tsaron, sun kama matasahin da zargin samun sa da kayan maye, inda yake boye da wasu basu sani ba, kafin kuma a kai shi kotu, ya ciro su yana yunkurin hadiye wa.

Wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki yana da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending