Connect with us

Labarai

A guji shafin bogi na Internet da ya ke ci gaba da yin katin zaɓe – INEC

Published

on

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta gargadi ‘yan ƙasa game da wata hanyar yin rajista katin zaɓe na bogi da a ke yi a shafukan internet.

Hukumar ta fitar da sanarwar ne a cikin wata sanarwa da kwamishinanta na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye, ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce, an ja hankalin hukumar ta INEC, zuwa wani shafin internet da ke kira ga ‘yan Najeriya da su yi rajistar katin zabe .

Shafin ya yi ikirarin cewa, gwamnatin tarayya ta amince da yin rijistar katin zabe a shafin, domi gujewa cunkoson jama’a a cibiyoyin rijistar, in ji sanarwar.

Hukumar ta kuma ce, duk da haka ta tabbatar da cewa, rukunin shafin internet ɗin ba shi da alaƙa da hukumar, domin haka al’umma su gujewa shafin.

Labarai

Rahoto: Mu nisanci abinda Allah Ya hana domin samun saukin rayuwa – Limamin Tukuntawa

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa a jihar Kano, Malam Ahmad Ali, ya ce, al’umma su duba tsakanin su da Allah tare da nisantar abinda ya hana, domin saukin tsadar rayuwa.

Malam Ahmad Ali, ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa wakilin mu na ‘yan Zazu,  Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, Karin bayani dangane da abinda hudubar da ya gabatar ta kunsa.

Akwai cikakken bayanin hudubar a muryar da ke kasa.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rubutu na da muhimmanci a mu’amalar bashi – Limamin Bompai

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke unguwar Bompai, SP Abdulkadir Haruna, ya ce, akwai bukatar mu rinka gudanar da mu’amalar bashi yadda addinin musulunci.

SP Abdulkadir Haruna, yana bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, bayar idar da Sallar Juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashi ya yi yunkurin cinye tabar Wiwin da aka kama shi da ita a hanyar kotu

Published

on

Ana zargin wani matashi ya yi yunkurin hadiye tabar Wiwi da miyagun kwayoyi da aka kama shi da ita a hanyar kotu.

Tunda fari jami’an tsaron, sun kama matasahin da zargin samun sa da kayan maye, inda yake boye da wasu basu sani ba, kafin kuma a kai shi kotu, ya ciro su yana yunkurin hadiye wa.

Wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki yana da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending