Connect with us

Labarai

KAROTA ta cafke wani matashi mai sojan-gona da hukumar ya na cusguna wa al’umma

Published

on

Hukuma mai kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta cafke wani matashi yana sojan-gona da hukumar, dai-dai lokacin da yake tsaka da tare motoci a kan titi sha biyu na daran ranar Litinin.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Nabulisi Abubakar kafar Na’isa ne ya tabbatar wa da manema labarai afkuwar lamarin.

Yana mai cewa, idan suka kammala binke a kan sa za su miƙa shi hannun jami’an Yansanda, domin faɗaɗa bincike tare da gurfanar da shi a gaban kotu domin fuskantar tuhuma.

Ya kuma ce, hukumar ta jima da samun rahoton yadda matashin yake amfani da yawunta, wajen cusgunawa al’umma, wanda sai a wannan karon dubunsa ta cika.

Matashin mai suna Lukman Abdullahi mai shekaru 27 mazaunin unguwar Sabon Gari, bayan kama shi ya bayyana cewa, shi ɗan Maiduguri ne, kuma yana amfani da kayan ne saboda jama’a su fahimci shi ma’aikacin hukumar ne.

Shugaban Hukumar ta KAROTA Baffa Babba Ɗan’agundi ya shawarci al’umma da su ci gaba da kai rahoton duk wani jami’in da suka ga yana karɓar cin-hanci domin ya fuskanci tuhuma.

Labarai

Rahoto: Mu nisanci abinda Allah Ya hana domin samun saukin rayuwa – Limamin Tukuntawa

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa a jihar Kano, Malam Ahmad Ali, ya ce, al’umma su duba tsakanin su da Allah tare da nisantar abinda ya hana, domin saukin tsadar rayuwa.

Malam Ahmad Ali, ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa wakilin mu na ‘yan Zazu,  Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, Karin bayani dangane da abinda hudubar da ya gabatar ta kunsa.

Akwai cikakken bayanin hudubar a muryar da ke kasa.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rubutu na da muhimmanci a mu’amalar bashi – Limamin Bompai

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke unguwar Bompai, SP Abdulkadir Haruna, ya ce, akwai bukatar mu rinka gudanar da mu’amalar bashi yadda addinin musulunci.

SP Abdulkadir Haruna, yana bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, bayar idar da Sallar Juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashi ya yi yunkurin cinye tabar Wiwin da aka kama shi da ita a hanyar kotu

Published

on

Ana zargin wani matashi ya yi yunkurin hadiye tabar Wiwi da miyagun kwayoyi da aka kama shi da ita a hanyar kotu.

Tunda fari jami’an tsaron, sun kama matasahin da zargin samun sa da kayan maye, inda yake boye da wasu basu sani ba, kafin kuma a kai shi kotu, ya ciro su yana yunkurin hadiye wa.

Wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki yana da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending