Connect with us

Labarai

Kotu ta sake tabbatar da Ruto a matsayin shugaban Kenya

Published

on

Kotun kolin Kenya, a safiyar Litinin, ta tabbatar da nasarar William Ruto a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan jiya.

An ayyana Ruto a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka kammala a kasar da ke gabashin Afirka.

Ya samu kashi 50.49 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada (7,176,141), inda ya doke abokin hamayyarsa, tsohon Firayim Minista Raila Odinga kuma shugaban kasar wanda ya samu kashi 48.85 (6,942,930) na kuri’un da aka kada.

Mista Ruto ya kuma samu mafi karancin kuri’u kashi 25 cikin dari a kananan hukumomi 39.

Sai dai Mista Odinga ya ki amincewa da sakamakon zaben yana zargin an tabka magudi, kuma ya garzaya kotu a sakamakon haka.

Hudu daga cikin mambobin hukumar zabe bakwai kuma sun ki tantance sakamakon zaben.

A hukuncin da ta yanke, kotun kolin ta yi watsi da karar da madugun ‘yan adawa, Raila Odinga ya shigar kan nasarar da Ruto ya samu a zaben.

Babbar jojin kasar, Martha Koome, ta karanta hukuncin a madadin sauran alkalai

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Labarai

Iyaye ku dai ma marawa ƴaƴan ku baya akan abinda suke yi da ya saɓawa doka – Mai unguwar Ja’en Jigawa

Published

on

Mai unguwar Ja’en Jigawa da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano Sani Muhammad, ya ce bai kamata a rinƙa samun wasu iyaye da ɗabi’ar nan ta marawa ƴaƴan su baya akan abinda yaran suke aikatawa na saɓawa Doka, domin gujewa abinda ka je ya dawo.

Mai unguwar ya bayyana hakan ne yayin zantwarsa da gidan rediyon Dala FM, a lokacin da yake tsokaci kan yadda ake samun wasu daga cikin iyayen yankin sa na marawa ƴaƴan su baya kan abinda suke yi na ba dai dai ba, lamarin da yake ƙara ƙara kangarar da tarbiyyar ƴaƴan tare da tayar da hankalin al’umma.

Mai unguwa Sani Muhammad, ya kuma ce matuƙar yaran ba za su zauna lafiya a cikin unguwa da al’umma ba, to kuwa za su rinƙa ɗaukar matakin miƙa yaran hannun jami’an tsaro mafi kusa, domin ɗaukar matakin da ya dace a kan su, wajen ganin sun sauke nauyin da aka ɗora musu.

Sani Muhammad, ya ƙara da cewa ko a baya bayan nan wasu matasa sai da suka yi yunƙurin yin abinda bai kamata ba, lamarin da yasa aka ɗauki mataki a kansu amma aka samu wasu daga cikin iyaye suka marawa yaran nasu baya, wanda hakan kan haifar da barazanar tsaro.

Continue Reading

Labarai

Matasa ku ƙara dagewa da neman Ilmin addini da na zamani – Dr. Abdallah Gadan Kaya

Published

on

Fitaccen malamin addinin Musluncin nan Dakta Abdallah Usman Umar, ya shawarci matasa da su ƙara mayar da hankali wajen neman ilmin addinin da na zamani, domin zama ababen koyi a tsakanin al’umma.

Dakta Abdallah Gadan Ƙaya, ya bayyana hakan ne ta cikin Tafsirin Al-ƙur’ani mai girma, da yake gabatarwa cikin wannan watan azumin Ramadana a jihar Gombe.

A cewar sa, “Akwai buƙatar matasa ku yi riƙo da ƙananan sana’o’in dogaro da kai, da za ku rinƙa biyawa kan ku kuɗin makaranta wajen neman ilimi domin kaucewa zama a cikin jahilci, “in ji shi”.

Dakta Abdallah, ya kuma yi kira ga shugabanni da su dukkan abinda ya dace wajen inganta makarantu a sassan ƙasar nan, domin ganin ɗalibai sun samu ingantaccen Ilmi.

Continue Reading

Trending