Labarai
Rahoto: Babu kudin da za a biya wanda aka rushe wa gini a Kantin Kwari ba – Baffa Babba

Shugaban hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, kuma daya daga cikin ‘yan kwamitin rusau, a kasuwar Kantin Kwari, Hon. Baffa Babba Dan-Agundi ya ce, babu wasu kudade da za a baiwa duk wanda aka rushe ginin da yayi kan magudanan ruwan kasuwar.
Baffa Babba, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il, ta waya dangane da rusau ake gudanarwa a kasuwar ta Kwantin Kwari a gin-ginen da aka yi su kan magudanan ruwa.
Akwai cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Daurin Boye
Mun kafa kwamiti domin rage farashin – Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti da zaiyi Duba kan hanyoyin shigo da abinci domin rage farashin sa da kaso 50.
Kwamitin dai dake karkashin mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima zai yi aiki ne da wasu ministoci, domin ganin an wadatar Nigeria da abinci.
Yayin jawabin sa, Sanata Kashim Shettima yace hakan wani bangare NE na kara inganta tattalin arziki da shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu ke kokari.

Labarai
Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.
A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Hangen Dala
Bamu da labarin kwankwaso zai koma APC – NNPP

Jamiyyar NNPP a Kano tace ba ta da masaniyar labarin da ake yadawa na cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na Shirin komawa jamiyyar APC.
Shugaban jamiyyar na Kano Honorable Hashimu Suleman Dungurawa ne ya bayyana hakan ta cikin Shirin siyasa hangen dala, na tashar Dala Fm.
Yace abin da ake yadawa zance ne mara tushe balle makama, a don haka al’umma suyi watsi da wannan labari.
Koda dai yace su na maraba da duk wani Mataki da Sanata Kwankwason ya dauka suna tare dashi.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su