Wasanni
Amuneke ya zama sabon mai horas da Zanaco FC

An nada tsohon dan wasan Super Eagles, Emmanuel Amuneke, a matsayin sabon mai horas da kungiyar Zanaco FC ta Zambia.
Amuneke, wanda ya taba zama mataimakin kocin Super Eagles, ana sa ran nan da kwanaki masu zuwazai isa kasar Afrika ta Kudu domin ya kulla kwantiraginsa.
Cikakkun bayanai na kwantiraginsa sun kasance cikin tsari a halin yanzu.
Amuneke yana da mutu’a sosai a Najeriya bayan ya jagoranci ‘yan wasan Golden Eaglets na Najeriya ‘yan kasa da shekaru 17 zuwa gasar cin kofin duniya na FIFA na 2015 a Chile.
Dan wasan mai shekaru 51 ya kuma samu tikitin zuwa kasar Tanzaniya a gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a Masar a shekara ta 2019 bayan shafe shekaru 39.
Ya kasance memba a kungiyar Super Eagles da ta lashe gasar cin kofin Afrika a shekarar 1994 a Tunisia.
A shekarar 2016 ne Zanaco ta lashe kofin gasar kasar Zambia.

Wasanni
Kano Pillars ta sayi Salisu Abdullahi

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Capital City da take a babban birnin tarayya Abuja wato Salisu Abdullahi
Salisu ya rattaba kwantaragin shekara daya da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya kuma sha alwashin yin aiki tukuru tare da yan wasan kungiyar, dan ganin kungiyar ta samu nasarori a gasar da zata buga ta cin kofin kwararru na Nigeria ta shekarar 2023 zuwa 2024.

Wasanni
Chelsea ta sayi Lavia daga Southampton

Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Southampton wato Romeo Lavia a kan kudi €58m.
Romeo Lavia, dan asalin kasar Belgium mai shekaru 19, ya rattaba kwantaragin shekaru bakwai da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.
Kafin komawar dan wasa Lavia kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Southampton wasanni 34.
“Ina farin cikin komawa ta kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, kuma komawar ta zo min kamar a mafarki, domin Chelsea kungiya ce da take da tarihi kuma kowanne dan wasa zai so ace yana buga wasa a Chelsea, kuma zan hada kai da abokan wasana dan ganin mun kai kungiyar mu ga babban mataki” a cewar Lavia.

Wasanni
Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta dauki sabbin yan wasa

A yunkurinta na tunkarar sabuwar kakar wasan gasar Firimiyar Nigeria wato NPFL ta shekarar 2023 zuwa 2024, Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sayi sabbin yan wasa guda uku domin yin garan bawul ga kungiyar.
‘Yan wasan dai sun hadar da Ibrahim Mustafah Yuga da Abubakar Ibrahim Babawo wayanda suka tawo daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Plateau United dake jihar Jos, sai kuma Abubakar Aliyu daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Wikki Tourists dake jihar Bauchi, sanarwar dai ta fito ta hannun mai magana da yawun kungiyar ta Kano Pillars Lurwanu Idris Malikawa.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano