Manyan Labarai
Rahoto: A sasauta mana domin mu mallafi shaguna – Mariri ‘yan Gwanjo

Kungiyar ‘yan Gwanjo da ke Mariri ‘yan itace, sun koka dangane da yanka shaguna wadanda suka fi karfin ‘yan kasuwar wurin.
Ma’ajin kungiyar, Bashir Hamza Mai Gwanjo, ya bayyana hakan, yayin zantawarsa da wakilin mu na Abubakar Sabo.
Akwai cikakken rahoton saurari wannan.

Hangen Dala
Yau shugaban kasa zai dawo daga Faransa

Bayan ziyarar aiki ta kusan mako biyu Zuwa kasar Faransa a yau litinin ake saka ran shugaban kasa zai dawo gida Nigeria.
Cikin sanarwar da hadimin shugaban kasar kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar ya ce kowa ne lokaci daga yanzu shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu zai sauka a Nigeria domin cigaban da harkokin mulkin kasar.

Manyan Labarai
Gobara ta ƙone tarin shaguna a kasuwar Kurmi da ke Kano – ACFO Saminu Yusuf

Hukumar kashe Gobara ta jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin babban daraktan ta Alhaji Sani Anas, ta tabbatar da ƙonewar shaguna guda shida ƙurmus a kasuwar Kurmi Jakara Ƴan Jagwal da ke jihar, sakamakon tashin Gobara.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikowa tashar Dala FM Kano, a ranar Juma’a 18 ga watan Afrilun 2025.
“Sashin mu na karɓar kiraye-kirayen gaggawa ya karɓi kiran gaggawa daga baturen Ƴan Sandan Jakara, wanda ya sanar da tashin gobarar a safiyar Juma’ar nan; ko da jami’an mu suka je wurin sun tarar wutar ta ƙone shaguna 6 ƙurmusu, da kuma wasu shaguna biyar da wani ɓangaren su ya ƙone, “in ji Saminu”.
Kazalika, Hukumar kashe Gobarar ta jihar Kano, ta ce jami’anta sun yi nasarar kashe wutar ba tare da ta tsallaka zuwa Maƙota ba, tare da ƙoƙarin tseratar da Miliyoyin Naira a lokacin.
ACFO Saminu Yusuf, ya kuma ce hukumar za ta yi duk mai yiyuwa domin ganon musabbin tashin gobarar, kasancewar ko a baya ma kimanin sati biyu da suka gabata, sun samu makamancin tashin wutar, ko da dai ya ce babu rasa rai ko kuma jikkata a tashin gobarar.

Hangen Dala
Kofar APC a bude take ga masu shiga – Abdullahi Abbas

Jamiyyar APC a Jihar Kano tace Kofar ta a bude take ga dukkanin masu son shigowa jamiyyar.
Shugaban jamiyyar na Kano Hon Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.
Abbas yace labarin dake yawo cewa akwai wadanda ke Shirin shigowa jamiyyar, su sani Kofar APCn a bude take tare da maraba ga dukkanin wadanda zasu shigo.
Koda dai Abdullahi Abbas yace shigowa APC ba zai hana tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa ba, koma kaucewa hukumar EFCC da ICPC.
A baya bayan nan ne dai aka rinka yada cewa mabiya jamiyyar NNPP kwankwasiyya na Shirin shiga jamiyyar APC tare da madugun ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su