Connect with us

Wasanni

Enyimba ta dauki dan wasa Elijah daga MFM FC

Published

on

Enyimba ta sanar da daukar dan wasan tsakiya Elijah Akanni daga kungiyar kwallon kafa ta MFM FC.

Akanni ya yanke alaka da MFM, biyo bayan ficewar Olukoya Boys daga gasar kwararrun kwallon kafa ta kasa a kakar wasan da ta wuce.

“Kungiyar kwallon kafa ta Enyimba ta cimma yarjejeniya kan siyan Elijah Akanni,” in ji wata sanarwa.

Zakarun NPFL har sau takwas, Enyimba na neman sake gina kungiyar bayan rashin nasarar da suka yi a kakar wasan da ta wuce.

Wasanni

Kano Pillars ta sayi Salisu Abdullahi

Published

on

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Capital City da take a babban birnin tarayya Abuja wato Salisu Abdullahi

Salisu ya rattaba kwantaragin shekara daya da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya kuma sha alwashin yin aiki tukuru tare da yan wasan kungiyar, dan ganin kungiyar ta samu nasarori a gasar da zata buga ta cin kofin kwararru na Nigeria ta shekarar 2023 zuwa 2024.

Continue Reading

Wasanni

Chelsea ta sayi Lavia daga Southampton

Published

on

Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Southampton wato Romeo Lavia a kan kudi €58m.

Romeo Lavia, dan asalin kasar Belgium mai shekaru 19, ya rattaba kwantaragin shekaru bakwai da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.

Kafin komawar dan wasa Lavia kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Southampton wasanni 34.

“Ina farin cikin komawa ta kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, kuma komawar ta zo min kamar a mafarki, domin Chelsea kungiya ce da take da tarihi kuma kowanne dan wasa zai so ace yana buga wasa a Chelsea, kuma zan hada kai da abokan wasana dan ganin mun kai kungiyar mu ga babban mataki” a cewar Lavia.

Continue Reading

Wasanni

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta dauki sabbin yan wasa

Published

on

A yunkurinta na tunkarar sabuwar kakar wasan gasar Firimiyar Nigeria wato NPFL ta shekarar 2023 zuwa 2024, Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sayi sabbin yan wasa guda uku domin yin garan bawul ga kungiyar.

‘Yan wasan dai sun hadar da Ibrahim Mustafah Yuga da Abubakar Ibrahim Babawo wayanda suka tawo daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Plateau United dake jihar Jos, sai kuma Abubakar Aliyu daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Wikki Tourists dake jihar Bauchi, sanarwar dai ta fito ta hannun mai magana da yawun kungiyar ta Kano Pillars Lurwanu Idris Malikawa.

Continue Reading

Trending