Ilimi
Da Duminsa: Kotu ta ce lallai ASUU ta koma bakin aiki

Kotun kolin masana’antu ta kasa ta umarci kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU, da ta janye yajin aikin da ta shiga na watanni kusan bakwai da ta shiga.
Mai shari’a Polycap Hamman ta bayar da umarnin dakatar da yajin aikin ne yayin da ta ke yanke hukunci a wata takardar da gwamnatin tarayya ta shigar na neman a tilasta wa malaman jami’o’in su koma bakin aiki har sai an warware musu bukatunsu na kyautata yanayin aiki.
Kotun ta yi amfani da sashe na 18 na dokar takaddamar ciniki da kuma bukatun kasa na daliban Najeriya da su amince da bukatar gwamnatin tarayya na neman umarnin hukunta malaman.

Ilimi
NECO ta saki sakamakon jarrabawar bana

Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta fitar da sakamakon 2023 na daliban da suka zana jarabawar tare da samun kashi 61.6 na wadanda suka samu Turanci da Lissafi.
Da yake fitar da sakamakon a ranar Talata, magatakardar hukumar, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce jimillar dalibai 1,196,985 ne suka zauna zana jarabawar.
Ya ce daga cikin jimillar dalibai da suka zauna jarabawar, 737,308 sun samu nasara da kiredit biyar zuwa sama, da suka hada da harshen Turanci da lissafi, wanda ke wakiltar kashi 61.60 cikin 100 na dalibai 1,196,985 kuma sun cancanci shiga jami’a

Addini
Abubuwan da ya kamata mu yi a lokacin da muke cikin fushi.

- Fushi daga shaidan yake
- Mu yawaita zama da Alwala da kuma ambaton Allah
- Mu guji daukar hukunci lokacin da muke cikin fushi .
A shafin sa na facebook, Falalu Dorayi yayi tsokaci kan abubuwan dake jawo fushi, da kuma hanyoyi kauce musu kamar haka
Tasirin fushi a zucivar Dan Adam na iva haifar da masifu da abubuwa marasa dadi iri iri, ciki harda kisan kai.
Duk Lokacin da Dan Adam yake cikin fushi ko wani vanayi na bacin rai,Tabbas wannan mutumin na samun bakuncin Shaidan kusa da zuciyarsa, kuma duk hukuncin da zai yi a wannan lokacin ba zai zamo mai inganci ba,ma’ana zai dauki hukunci mara dadi.
Idan muka samu kanmu a irin wannan yanayin Ma’aiki Rasulullah (SAW) Ya bamu mafita:
- Mu daura Alwala
- Mu yawaita fadin “A’udhu billahi minashaytaan-ir-rajeem”
- Idan a tsaye muke mu zauna, idan bamu daina fushin ba kuma mu kwanta.
Kada mu biyewa zuciya, mu kasance masu hakuri.
Rahoto: Koyi da halayen Annabi ne nuna tsantsar kaunar sa – Limamin Tukuntawa
Ubangiji Yana son masu hadiye fushi da yafiya lokacin da aka fusata su.
Mu duba; (Ali Imran 3:134)
Allah Yasa mu dace

Ilimi
Ba Aiki Ba Biya: Mu na nan a kan bakar mu – Gwamnati

Yayin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ke gudanar da zanga-zangar lumana a faɗin jami’o’in ƙasar nan, domin nuna rashin jin daɗinsu game da rashin biyansu albashin watannin da suka kwashe suna yajin aiki, gwamnatin ta ce, ba za ta biya malaman albashin aikin da ba su yi ba.
Ministan ilimin ƙasar Malam Adamu Adamu ne ya bayyana haka ranar Laraba, bayan taron majalisar zartarwa da shugaban ƙasar ya jagoranta a fadar gwamnatin da ke Abuja.
Yayin da yake martani game da iƙirarin da shugaban ASUU ya yi na cewa gwamnati na son mayar da malaman jami’ar ma’aikatan wucin-gadi, ministan ya ce gwamnatin ba ta da wannan niyyar.
“An janye yajin aiki, kuma gwamnati ta biyasu haƙƙin iya aikin da suka yi. Ina tunani wannan shi ne matsayin gwamnati, cewa ba wanda za a biya albashin aikin da bai yi ba, sun yi aiki na kwanaki, kuma gwamnati ta biya su haƙƙinsu kwanakin da suka yi”, in ji Adamu Adamu.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano