Connect with us

Manta Sabo

Da Duminsa: Majalisar Dattawa ta amince da nadin Alkalin Alkalai

Published

on

Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Mai Shari’a, Olukayode Ariwoola, a matsayin sabon Alkalin Alkalai (CJN) na kasa.

Wannan ci gaban dai ya biyo bayan tantance shi da kwamitin koli ya yi na zauren majalisar dattawa a ranar Laraba.

A yayin tantancewar, Mai shari’a Ariwoola ya amsa tambayoyin da Sanatoci su ka yi masa.

Manta Sabo

Kotu ta wanke tare da sallamar shugaban kwamitin samar da tsaro na Ƙofar Na’isa Abdullahi Isma’il da mataimakin sa

Published

on

Kotun Magistrate mai lamba 25 dake zamanta a unguwar No-man’s-land, ƙarkashin Jagorancin mai Shari’a Hajiya Halima Wali, ta wanke tare da sallamar shugaban kwamitin samar da tsaro na unguwar Kofar Na’isa Abdullahi Isma’il, da mai taimaka masa Baffa Muhammad.

Ƴan kwamitin dai da kotun ta wanke an zarge su ne da halaka wani matashi mai Suna Abba Mai laƙabin Ɗan Snake.

Tashar Dala FM Kano, ta labarto cewar hakan na zuwa ne bayan da kotun ta samu shawarwari daga ofishin babban lauyan gwamnatin jihar Kano.

A baya dai an zarge su da halaka Ɗan Snake, ne bayan da ya shafe kusan watanni shida ana memansa ba’agan shi ba.

Daga bisani ne dai aka samu gawarsa a cikin wani kududdifi dake unguwar Kofar Na’isa a karamar hukumar Gwale dake jihar ta Kano, kamar yadda wakilinmu Aminu Abdu Bakanoma ya rawaito.

Continue Reading

Manta Sabo

Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata, ta tabbatar wa iyalan Sharu Ilu Rami a Kano

Published

on

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a sakatariyar Audu Baƙo a jihar Kano, ta yi hukunci akan shari’ar da dattijon nan Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata ya ɗaukaka, akan wani babban rami da aka yi taƙaddama akansa da ke unguwar Gwammaja a jihar.

Tunda fari dai dattijon ya ɗaukaka ƙarar ne akan hukuncin da babbar kotun kotun jaha ƙarkashin mai Shari’a Justice Usman Na Abba, ta yi, inda ta mallaka wa iyalan marigayi Sharu Ilu ramin, lamarin da dattijon ya ɗaukaka ƙarar.

Sai dai kuma a zaman kotun na yau Laraba, alkalin da ya jagoranci yanke hukuncin a kotun ɗaukaka ƙarar Justice U-A Musalli, ya kori ƙarar dattijon, tare kuma da tabbatar da hukuncin kotun ƙasa, ma’ana dai a baiwa magada iyalan marigayi Sharu Ilu ramin kamar yadda aka yi hukuncin baya a kotun ƙasan.

Bayan fitowa daga kotun ne wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u, ya yi duk mai yiyuwa dan ji daga ɓangaren lauyar Dattijo Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata, mai suna Veronika, sai dai ta ce ba abinda za ta ce, a nan ne ya wai-wayi guda daga cikin lauyoyin waɗanda akayi ƙara mai suna Yahya Y Sharif, wanda ya ce daman haka suka yi tsammani, kuma gashi gaskiya tayi halin ta.

Daga bisani dai kotun ta ce a shirye take da ta baiwa kowanne bangare kwafin hukuncin, kuma duk wanda bai gamsu da hukuncin ba yana da dama ya wuce kotun gaba.

Aƙalla dai an shafe sama da shekaru biyar ana taƙaddamar ramin dake unguwar Gwammaja a Kano.

Continue Reading

Manta Sabo

Kotu ta aike da ƴan Daudu 5 gidan yari kan zargin kai hari ofishin Hisbah a Kano.

Published

on

Babbar kotun shari’ar muslunci dake zamanta a shahuci ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Muhammad Sani Ibrahim, ta aike da wasu matasa 5 gidan gyaran hali zuwa ranar 15 ga watan gobe.

Tun da fari gwamnatin jahar kano ce ta gurfanar da su bisa zargin sun haɗa baki da yin wasan Bori, ɓarna da kuma lalata kayan gwamnati.

Kunshin tuhumar ya bayyana cewar matasan sun haɗa baki sun kai farmaki ofishin Hisbah dake unguwar Bachirawa ƙarshen kwalta, inda suka ragargaje motar hukumar Hisbar yankin suka kuma farfasa gilashin tagar ofishin Hisbar.

Matasan sun hadar da Nasiru Hamisu, da Aminu Sani, da kuma Auwal Haruna, sai Auwal Tasi’u sai kuma Musa Umar.

Yayin da aka karanta musu tuhumar a gaban kotun matasan sun musanta, lauyansu Barister Aliyu Bashir Buba ya roki kotun da ta sanya su a hannun beli, sai dai kuma lauyan gwamnati Barister Zaharaddin Mustafa ya yi suka.

Lauyan gwamnati ya bayyana cewar kotu uwar kowa ce, kuma yana tsoron kada a bayar da belin wani abu ya biyo baya tunda matasan sun tunzura mutanen unguwar Bachirawar Tukwane.

A nan ne kotun ta aike da matasan su biyar gidan gyaran hali zuwa ranar 15 ga watan gobe.

Wakiliu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewar laifukan da ake tuhumar matasan sun saɓa da sashi na121, da na 277 da kuma na 364, sai kuma sashi na 386 na kundin Penal code.

Continue Reading

Trending