Connect with us

Wasanni

Na kagu mu tunkari Algeria a wasan sada zumunci – Mai horas da Super Eagles

Published

on

Mai horas da tawagar Super Eagles, Jose Peseiro ya kagu ya ga ya fafata a wasan sada zumunta da kungiyar za ta yi da Algeria.

Peseiro dan Portugal, ya sake hadewa da tawagarsa bayan wasan karshe da suka yi a Sao Tome da Principe a watan Yuni.

A halin yanzu dai Super Eagles na can a Constantine suna shirye-shiryen buga wasanni biyu na sada zumunta da Desert Foxes.

Peseiro ya dauki nauyin atisayen ne a ranar Talata tare da mataimakan sa.

Tsohon kocin Venezuela da Saudi Arabiya ya ji dadin yin aiki tare da ‘yan wasansa wajen atisayen tunkarar wasannin sada zumunta.

Ya ce “Ina jin daɗin dawowa tare da tawagar! Saurari mako na aiki tukuru da horo, kafin wasan sada zumunci da Algeria
Mu tafi!, ” In ji Peseiro ta shafinsa na tweeter da ya wallafa.

Peseiro zai jagoranci tawagarsa a wasan sada zumunta na farko da Algeria a gidan ta a filin wasa na Mohamed Maloiul, Constantine ranar Juma’a.

Super Eagles da Desert Foxes za su fafata a filin wasa na Miloud Hadefi, Oran, mako mai zuwa ranar Talata.

Wasanni

Kano Pillars ta sayi Salisu Abdullahi

Published

on

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Capital City da take a babban birnin tarayya Abuja wato Salisu Abdullahi

Salisu ya rattaba kwantaragin shekara daya da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya kuma sha alwashin yin aiki tukuru tare da yan wasan kungiyar, dan ganin kungiyar ta samu nasarori a gasar da zata buga ta cin kofin kwararru na Nigeria ta shekarar 2023 zuwa 2024.

Continue Reading

Wasanni

Chelsea ta sayi Lavia daga Southampton

Published

on

Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Southampton wato Romeo Lavia a kan kudi €58m.

Romeo Lavia, dan asalin kasar Belgium mai shekaru 19, ya rattaba kwantaragin shekaru bakwai da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.

Kafin komawar dan wasa Lavia kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Southampton wasanni 34.

“Ina farin cikin komawa ta kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, kuma komawar ta zo min kamar a mafarki, domin Chelsea kungiya ce da take da tarihi kuma kowanne dan wasa zai so ace yana buga wasa a Chelsea, kuma zan hada kai da abokan wasana dan ganin mun kai kungiyar mu ga babban mataki” a cewar Lavia.

Continue Reading

Wasanni

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta dauki sabbin yan wasa

Published

on

A yunkurinta na tunkarar sabuwar kakar wasan gasar Firimiyar Nigeria wato NPFL ta shekarar 2023 zuwa 2024, Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sayi sabbin yan wasa guda uku domin yin garan bawul ga kungiyar.

‘Yan wasan dai sun hadar da Ibrahim Mustafah Yuga da Abubakar Ibrahim Babawo wayanda suka tawo daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Plateau United dake jihar Jos, sai kuma Abubakar Aliyu daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Wikki Tourists dake jihar Bauchi, sanarwar dai ta fito ta hannun mai magana da yawun kungiyar ta Kano Pillars Lurwanu Idris Malikawa.

Continue Reading

Trending