Connect with us

Wasanni

Ndidi ba zai fafata ba a wasan Super Eagles da Algeria

Published

on

Dan wasan tsakiya na Leicester City, Wilfred Ndidi, ba zai buga wasan sada zumunci da Najeriya za ta fafata da Algeria sakamakon rauni da ya samu a kafarsa.

A cewar majiyoyin sansanin, Ndidi, ya sami rauni a wajen daukar horo a ranar Laraba.

Dan wasan mai shekaru 24 yana iya komawa kulob dinsa a Ingila a wannan makon, domin ci gaba da jinya kan raunin da ya ji.

Tsohon dan wasan KRC Genk bai buga karshen kakar wasa ta bara ba, bayan ya samu rauni, yayin da ya ke taka leda a Leicester City a gasar UEFA Europa Conference League da Stade Rennes a watan Maris.

A karshe ya buga wa Super Eagles wasa a zagaye na biyu da kungiyar Carthage Eagles ta Tunisia a gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2021 a Kamaru.

Mai horas da Super Eagles, Jose Peseiro, yanzu yana da ‘yan wasan tsakiya guda uku: Raphael Onyedika, Frank Onyeka da kuma Alex Iwobi wadanda za su buga wasan sada zumuncin.

Wasanni

Kano Pillars ta sayi Salisu Abdullahi

Published

on

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Capital City da take a babban birnin tarayya Abuja wato Salisu Abdullahi

Salisu ya rattaba kwantaragin shekara daya da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya kuma sha alwashin yin aiki tukuru tare da yan wasan kungiyar, dan ganin kungiyar ta samu nasarori a gasar da zata buga ta cin kofin kwararru na Nigeria ta shekarar 2023 zuwa 2024.

Continue Reading

Wasanni

Chelsea ta sayi Lavia daga Southampton

Published

on

Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Southampton wato Romeo Lavia a kan kudi €58m.

Romeo Lavia, dan asalin kasar Belgium mai shekaru 19, ya rattaba kwantaragin shekaru bakwai da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.

Kafin komawar dan wasa Lavia kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Southampton wasanni 34.

“Ina farin cikin komawa ta kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, kuma komawar ta zo min kamar a mafarki, domin Chelsea kungiya ce da take da tarihi kuma kowanne dan wasa zai so ace yana buga wasa a Chelsea, kuma zan hada kai da abokan wasana dan ganin mun kai kungiyar mu ga babban mataki” a cewar Lavia.

Continue Reading

Wasanni

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta dauki sabbin yan wasa

Published

on

A yunkurinta na tunkarar sabuwar kakar wasan gasar Firimiyar Nigeria wato NPFL ta shekarar 2023 zuwa 2024, Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sayi sabbin yan wasa guda uku domin yin garan bawul ga kungiyar.

‘Yan wasan dai sun hadar da Ibrahim Mustafah Yuga da Abubakar Ibrahim Babawo wayanda suka tawo daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Plateau United dake jihar Jos, sai kuma Abubakar Aliyu daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Wikki Tourists dake jihar Bauchi, sanarwar dai ta fito ta hannun mai magana da yawun kungiyar ta Kano Pillars Lurwanu Idris Malikawa.

Continue Reading

Trending