Connect with us

Labarai

Zamu gurfanar da Farfesar da ta lakadawa jami’ar mu duka – IGP Usman

Published

on

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP, Usman Alkali Baba, ya yi Allah-wadai da mummunan harin da aka kai wa wata jami’ar su mai suna Insifekta Teju Moses.

Shugabar wata makaranta Farfesa Zainab Duke Abiola da ma’aikatan gidanta da suka hada da ‘yar aikin gidan ta Rebecca Enechido da kuma wani namiji da ake zargi sun yi wa Teju dukan tsiya.

Wata sanarwa a ranar Alhamis ta hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, Muyiwa Adejobi ta sanar da cewa an kama Zainab da Rebecca.

Zainab, wata lauya, mai fafutukar kare hakkin dan Adam, da sauran su sun yi mata duka a ranar Talata a gidanta da ke Garki, Abuja.

Bidiyon da ke nuna Insifekta Teju tana jin zafi, tare da zubar da jini, yana yaduwa a shafukan sada zumunta.

Adejobi ya sanar da cewa IGP din ya bayar da umarnin gurfanar da wadanda ake zargin da ake tsare da su cikin gaggawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Labarai

Ranar ‘yan jaridu ta duniya: Aljanu na satar labarai daga sama – Danfodio

Published

on

Masanin harkokin aljanu a jihar Kano, Abdullahi Idris Danfodio ya ce, aljanu na satar labarai daga sama domin fada wa al’umma.

Abdullahi Idris Danfodio, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Akwai cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Da zarar PI ta fashe za mu yi abinda za mu taimaka wa mutane – Matashi

Published

on

Wani matashi a jihar Kano, Auwal Muhammad Musa, mai jiran fashewar PI ya ce, da zarar ta fashe za su gudanar da abubuwan da za su taimakawa al’umma.

Auwal Muhammad, ya bayyana, ya bayyana hakan ne, yayin zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matasa masu jiran fashewar PI na fama da matsalar damuwa – Masani

Published

on

Wani masani da ke karatun babban Digiri a jami’ar Bayero, bangaren nazarin halayyar Dan Adam a jihar Kano, Shu’aibu Lawan Matawalle, ya ce, akwai damuwa ga matasan da ke jiran fashewar PI, domin babu wanda yake samun kudi haka kawai ba tare da yayi kasuwanci ba.

Shu’aibu  Matawalle, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo, dangane da yadda matasa ke jiran fashewar PI.

Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Trending