Connect with us

Siyasa

Rikicin Jam’iyya: Idan PDP ta isa ta kore ni daga jam’iyyar – Wike

Published

on

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya kalubalanci kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP na kasa cewa da ta dakatar da shi daga jam’iyyar.

Hakan ya biyo bayan tattaunawar da aka yi a cikin jam’iyyar na cewa babu wanda zai kai jam’iyyar, kuma za a iya dakatar da shi.

Gwamnan ya ci gaba da tofa albarkacin bakinsa kan wasu jiga-jigan jam’iyyar, tun bayan kiran da ya yi a kan shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu da ya yi murabus.

A kwanakin baya ne Wike, ya jagoranci wasu jiga-jigan jam’iyyar suka fice daga majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, inda ya dage cewa sai Ayu ya tafi.

Da yake magana a wata tattaunawa ta kai tsaye a kafafen yada labarai a Fatakwal ranar Juma’a, Gwamna Wike ya ce, “Ina rokonsu a yau, kada su bata lokaci. Su kira taron kwamiti su ce Gwamnan Jihar Rivers, an dakatar da kai daga jam’iyyar.

“Duk abin da kuka ga kuna ɗauka. Sun san abin da zan yi. In ji Wike

 

Hangen Dala

Gaya Ajingi Albasu:- Dan majalisa ya raba kayan abinci

Published

on

Dan majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu Dakta Ghali Mustafa Fanda ya fara rabon tallafin kayan abinci ga al’ummar kananan hukumomin uku.

 

Yayin rabon tallafin kayan abincin, Dakta Ghali Mustafa yace yayi rabon tallafin ne domin fara sauke nauyin al’ummar da yake wakilta.

 

” Wannan tallafi zamu bayar da shi ne domin fara sauke nauyin al’ummar da suka zabe mu, kuma wannan shi ne karon farko, kuma yayi daidai da bukatar al’umma a yanzu, shiyasa muka fara da tallafin kayan abinci”.

 

“A cikin wannan tallafi mutane kimanin dubu ashirin ne zasu amfana, wanda zamu bayar da buhunan Shinkafa da Gero da Garin masara.”

 

Haka kuma ɗan majalisar ya bayar da tallafin Naira miliyan ashirin ga matasan kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu.

 

Sai kuma ɓangaren dalibai mata, wanda shima a yau dan majalisar ya dauki nauyin karatun dalibai mata guda 60 a bangaren lafiya.

 

Haka kuma cikin jawabin nasa Hon Ghali ya kuma ce nan gaba kadan zai bayar da tallafin taki ga manoma, da kuma farfaɗo da dukkanin rijiyon burtsatse na kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu a wani mataki na samar da ruwan sha.

 

Da yake nasa jawabin mataimakin gwamnan Kano Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo wanda ya samu wakilcin mai baiwa Gwamna Shawara kan harkokin siyasa Hon Sunusi Surajo Kwankwaso kira yayi ga sauran wakilan al’umma da suyi koyi da Dakta Ghali Mustafa Fanda wajen ayyukan alkhairi da kuma jin kan al’umma.

 

Haka kuma Hon Sunusi Surajo ya yabawa dan majalisar bisa bayar da tallafin ga ƙananan hukumomin uku.

 

Taron dai wanda ya gudana a cikin Islamic Centre na karamar hukumar Gaya ya samu halartar manya, da kuma jagororin yankunan uku, kuma nan take Dan majalisar Tarayya Dakta Ghali Mustafa ya fara rabon tallafin

Continue Reading

Hangen Dala

Shugaban kasa ya bayar da umarnin bude Boda

Published

on

Shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin bude iyakokin kasar nan.

Cikin sanarwar da ya fitar shugaban ya ce duk wata iyaka dake tsakanin Nigeria da jamhuriyar Nijar a gaggauta bude ta.

Karin bayani na nan tafe…

Continue Reading

Hangen Dala

An gurfanar na Ramat a gaban kotu

Published

on

Wasu yan jam,iyyar NNPP anan kano sun shigar da karar wani tsohon shugaban karamar hukuma.

Mutanen dai sun yi karar hon Abdullahi Garba Ramat tsohon shugaban karamar hukumar Ungogo, a gaban babbar kotun shariar muslinci ta birni.

Masu karar suna zargin Ramat da laifin tayar da hankalin al,imma ta hantar gayyato wasu yandaba suka tare musu hanya a lokacin yakin neman zabe sai dai Ramat din ya musanta zargin.

Mai sharia Ibrahim Sarki Yola ya aike da su wajen yansanda don a fadada bincike.

Alhaji Abubakar Iliyasu shine jagoran masu karar ya bayyana mana matsayarsu

Yanzu haka yansandan shahuci sun bukaci masu kara da su kawo gamsassun hujjoji akan da,awarsu.

Continue Reading

Trending