Manyan Labarai
Za mu horas da ma’aiakatan wucen gadi sama da miliyan 1 – INEC
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, ta ce, za ta horas da ma’aikatan wucin gadi har su 1, 400,000.
Babban Daraktan Cibiyar hulda da Manema Labarai na Hukumar, Dr. Sa’ad Umar Idris ne ya bayyana hakan game da muhimman batutuwan da suka shafi Kundin Zaben 2022 da Shirye-shirye da Tsare-tsaren hukumar don tunkarar babban zaben 2023.
A cewar Babban Daraktan za a gudanar da tarukan horas da jami’an zaben ne da cikakken kudurin tabbatar da yin zabe mai ‘yanci kuma cikin gaskiya da adalci a 2023.
Sa’ad Idris ya kuma ce, cibiyarsu ta dukufa wajen sauke nauyinta na tabbatar da ganin dukkan ma’aikatan wucin gadin sun samu ingantaccen horo kuma mai aminci.
“Za mu horas da Jami’an Duba-aikin Manyan Turawan Zabe kimanin 17,685 da Manyan Turawan Zabe wato Presiding Officers da Mataimakan Manyan Turawan Zabe (Assistants Presiding Officers) 707,384; sai Jami’an Tattara Sakamako (Collation Officers) 11,083; da Kwararrun Jami’ai (Registration Area Technical Officers) kimanin 12,991 da Jami’an Tsaro kimanin 20,000 da Manajojin kula da Cibiyoyin Zabe (Registration Area Centres Managers) 6,009 .”
Manyan Labarai
Wasu ɓata gari sun sace kayan sautin wani masallacin Juma’a a Kano
Al’ummar garin Kumbotso a jihar Kano sun wayi gari da ganin yadda wasu ɓata gari suka sace kayayyakin sautin da ake jin ƙarar kiran Sallah, a babban masallacin Juma’ar garin, al’amarin da ya sanya su a cikin damuwa.
Na’ibin limamin masallacin juma’ar mai suna Ibrahim Magaji Bello, ya shaidawa Dala FM Kano cewar, ɓata garin sun shiga masallacin ne a cikin daren Asabar, inda suka yi awon gaba da kayayyakin fitar da sautin bayan da suka farke ƙofar masallacin.
“Daga cikin kayayyakin da ɓata garin suka sace akwai baturan Fitilun da ke amfani da hasken Rana, da na’urar da ke taimaka wa wajen fitar da sauti, da wayar Na’ibin limamin masallacin da dai sauran su, “in ji shi”
Ibrahim Magaji ya kuma ce sace kayayyakin sautin ya sa yanzu haka ta kai ga ba’a jin sautin kiran Sallah, daga unguwanni daban-daban, da suka haɗar da garin na Kumbotso, da Rigafada, da Chalawa, da sauran wasu unguwanni, domin yanzu mutane suna makara sosai idan za su yi Sallah a masallacin.
“Muna kira ga gwamnati, da dukkanin masu hali da su taimaka su kawo mana ɗauki, domin ganin an sayi wasu kayan sautin a sanya a masallacin, domin ƙara ciyar da addinin Musulunci gaba, “in ji Ibrahim”.
Ya kuma ƙara da cewar tun bayan faruwar lamarin ne suke ta cigiyar waɗanda suka yi aika-aikar wajen zuwa su karɓi kayan su da suka manta yayin aikin nasu.
Ya ci gaba da cewa, “Daga cikin kayayyakin da ɓata gari suka manta akwai Pinches, abun da ake cire Ƙusa, ko kuma Kwaɗo, da Filayar su, da wasu kayayyaki, “in ji Na’ibin”.
Manyan Labarai
Gwamnatin Kano ta kulle ofishin kamfanin jiragen sama na Max Air da na Ɗantata and Sawoe a jihar
Gamnatin jihar Kano ta rufe ofishin kamfanin sufurin jiragen sama na Max air da na Dantata and Sawoe a nan Kano, sakamakon harajin da take bin kamfanonin.
Shugaban hukumar tattara haraji ta jihar Kano Dakta Zaid Abubakar, ne ya bayyana hakan bayan kulle kamfanonin biyu a ranar Litinin.
Zaid, wanda Daraktan Bibiyar bashi da tursasawa wajen karɓo bashin harajin da Gwamnatin Kano ke bi, Ibrahim Abdullahi ya wakilta, ya ƙara da cewar hukumar ta tattara haraji ta jihar Kano tabi duk matakan da ya kamata kafin daukar wannan matakin.
“Dole ce ta sa hukumar ɗaukar wannan mataki na rufe kamfanonin da wuraren da ke gujewa biyan haraji a jihar Kano, “in ji Ibrahim Abdullahi”.
Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar hukumar ta ce za ta ci gaba da bun duk matakan doka akan masu ƙin biyan harajin a fadin jihar Kano.
Manta Sabo
Kotu ta hana duk wata kafar yada labarai yin labarin da ya shafi Auwalu Danladi Sankara da Taslim Baba Nabegu.
Babbar kotun jaha mai lamba 4 karkashin jagorancin mai Shari’a Usman Na Abba ta yi hani ga duk wasu Jami’an Ƴan sanda ko na duk wata hukuma ta daban daga gayyata ko tsangwama, ko kuma bincike ko kamawa, ta kowace siga ga kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa Auwalu Ɗanladi Sankara.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kotu ta wanke Auwalu Sankara daga zargin mu’amala ko alaƙa da juna tsakanin mai ƙara da Taslim Baba Nabegu har zuwa lokacin sauraran ƙarar.
Kotun ta kuma amince da rokon da wani lauya mai suna Barrister I.C Ekpinovi ya yi amadadin mai kara Auwalu Danladi Sankara wanda ya yi karar Nasiru Buba.
Mai karar ta bakin lauyansa ya bayyana wa kotun rokonsa inda ya roki kotun da ta dakatar da wanda ake kara ko dai shi da kansa ko kuma ƴan korensa daga ci gaba da yaɗa wata magana wadda wata babbar kotun Shari’ar Muslunci da ke Kano ta rufe.
Mai Shari’a Usman Na Abba ya ayyana cewar ko dai wanda aka yi kara ko yan korensa ko kuma wasu wakilansa, da a dai na yaɗa waccan magana har zuwa lokacin da kotun za ta saurari kowanne ɓangare.
Kotun ta ayyana cewar ta yi hani ga duk wata kafa ta yada labarai ko dai Rediyo ko Talabijin, ko shafukan sada zumunta da kafar Intanet da duk wata kafa wadda take iya sadar da labarai, daga yaɗa labaran da suka shafi Auwalu Ɗanladi Sankara da Taslim Baba Nabegu.
A ranar Talata ne dai gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar Namadi ya bayyana mayar da Auwalu Ɗanladi Sankara muƙamin sa na Kwamishinan ayyuka na musamman a jihar, bayan da kotu ta wanke shi daga zargin da hukumar Hisbah ta Kano, ta yi masa kan zargin baɗala da wata matar aure.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa kotun ta kuma sanya ranar 28 ga wannan watan na Nuwamba dan sauraron kowane ɓangare akan shari’ar.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su