Connect with us

Wasanni

Mbappe ba na siyarwa ba ne – Mai horas da PSG

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain, Christophe Galtier, ya mayar da martani kan rade-radin da ake yi na cewa tauraron dan wasansa Kylian Mbappe zai bar kungiyar.

Ya yi watsi da rahotanni bayan da aka ce Mbappe ya bukaci barin kungiyar, ya na mai cewa dan wasan ya samu mafi kyawun amsar rade-radin da aka yi ta hanyar zura kwallo a wasansu na gasar cin kofin zakarun Turai a daren Talata.

Wani rahoto daga jaridar Marca ta kasar Sipaniya ya bayyana a ranar Talata, ya na mai cewa dan wasan na Faransa mai shekaru 23 ya na sha’awar barin PSG, duk da cewa ya kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar a farkon wannan shekarar.

Mbappe ya zura kwallo a wasan da su ka buga gasar cin kofin zakarun Turai da Benfica a daren jiya kuma ya ci wa zakarun Faransa kwallo a wasan da suka tashi 1-1.

Galtier ya musanta jita-jitar bayan wasan, yana mai cewa, “Ba zan iya yin tsokaci a kai ba,” in ji shi.

“Saboda haka, Kylian ya ba da amsa mai kyau: ya kasance mai zura qwallo; zai iya zura kwallo ta biyu. Ya washe hakora bayan wannan mugun takalmi. Ina ganin Kylian, wanda ya ba da wani martani ga wannan jita-jita.

“Na ga abin mamaki cewa [jita-jita] ta fito ‘yan wasu lokuta kafin irin wannan muhimmin wasa ga kulob din.”

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending