Connect with us

Lafiya

Dattijo dan shekara 67 da aka kulle tsirara sama da shekaru 20 ya shaki iskar ‘yanci

Published

on

Jami’an ‘yan sanda a karamar hukumar Kaduna ta Arewa, sun gano wani Dattijo mai shekaru 67, mai suna Ibrahim Ado, wanda aka kulle a daki sama da shekaru 20.

DSP Mohammed Jalige, mai magana da yawun rundunar, ya ce ‘yan sandan sun ceto mutumin ne a ranar Laraba.

A cewarsa, “An gano mutumin ne tsirara kuma an kulle shi a wani daki a wani gida da ke hanyar Bayajidda a cikin garin Kaduna. Mazauna gidan sun gudu a lokacin da tawagar ‘yan sanda suka isa gidan.”

Jalige ya bayyana cewa za a gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin lamarin.

A cewar wani ganau, jami’an kula da muhalli sun ziyarci gidan a safiyar Laraba, domin duba wasu abubuwan sha da aka ajiye a gidan, amma sun gano wani mutum a kulle a daki.

Ya kara da cewa, a cewar wata majiya, an tsare mutumin a dakin sama da shekaru 20.

Ya ce jami’an kula da muhalli sun kai rahoto ga sashin ‘yan sanda, kuma kwamishinan ‘yan sandan ya umarci jami’an da su kubutare wanda abin ya shafa.

Lafiya

Ku rinƙa ziyartar Asibiti ana muku gwaje-gwajen fitsari da Jini domin sanin halin da ƙodar ku take ciki – Likita

Published

on

An shawarci al’umma da su rinƙa ziyartar Asibiti akai akai wajen duba lafiyar su, ta hanyar yin gwaje-gwajen fitsari da jini domin sanin halin da kodar su ke ciki.

Dakta Muhajid Sunusi Rabi’u ne ya bayyyana hakan yayin ganawarsa da Dala FM, lokacin da suke aikin gwaje-gwajen fitsari da jini, kyauta a ɗaya daga cikin makarantu masu zaman kan su a nan Kano.

Dakta Mujaheed ya kuma ce sun gudanar da aikin ne a wani ɓangare na bikin ranar ƙoda ta Duniya, wadda aka ware duk ranar Alhamis ta mako na biyu na kowanne watan Maris domin gudanar da bikin ranar.

Continue Reading

Lafiya

Za’a yiwa kusan yara miliyan 3 rigakafin cutar shan Inna a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano tace kusan Yara miliyan 3 za’ayiwa rigakafin cutar shan inna a kananan hukumomin jihar nan 44, duba da samun ɓurɓushinta da kaso 65, a jihar ta Kano.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da rigakafin cutar shan innar a yau Alhamis, wanda za’a kwashe kwanaki 4 ana gudanarwa a Kano.

Dakta Abubakar Labaran ya ce duba da shigowar zafin akwai buƙatar al’umma su kula da alamomin cutar sankarau, duk da gwamnati ta yi shirin bayar da agajin gaggawa, kamar yadda tashar Dala FM Kano ta rawaito.

Ma’aikatar lafiyar ta jihar Kano dai ta ce za’a ci gaba da gudanar da sauran rigafin, domin bai wa yaran jihar Kano kariya daga cututtuka masu yaɗuwa.

Continue Reading

Lafiya

Dokar tilasta gwajin lafiya kafin aure ta tsallake karatu na biyu a majalisar dokokin Kano

Published

on

Rahotanni na bayyana cewar majalisar dokokin jihar Kano, ta yi karatu na biyu a kan kudirin dokar tilasta wa masu niyyar yin aure yin gwajin cutar kanjamau, da na cutar hanta da kuma duba kwayoyin jini wato Sikila, gabanin daura aure.

Ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Takai, Hon.Musa Ali Kachako, shin wanda ya kawo kudirin dokar, ya bayyana cewa, jihar Kano na fama da matsalolin lafiya daban-daban da suka hada da cutar kanjamau saboda mutane kan yi aure ba tare da an duba lafiyarsu ba, hakan ne ma ya sa ya kai ƙudirin.

Kachako, ya ce, ƙudirin dokar idan har aka amince da shi, zai ceci rayuka da dama tare da dakile yaɗuwar cututtuka masu barazana ga rayuwar al’umma, kamar yadda jaridar Kadaura24 ta rawaito.

Da yake nuna goyon bayansa kan ƙudirin Ɗan majalisa Hon. Aminu Sa’ad, mamba mai wakiltar mazabar Ungogo, ya ce, jihohin Jigawa, Katsina da Kaduna sun zartar da irin wannan kudiri domin magance kalubalen kiwon lafiya da suke fuskanta.

Ya ce tilas ne Kano da ke da yawan al’umma a kasar nan ta zartar da kudirin dokar, domin kare lafiyar ‘yan jiharta ta hanyar samar da gwaje-gwaje kafin aure domin dakile yaduwar cututtuka, kamar cutar hanta, da sauran cututtuka.

Continue Reading

Trending