Siyasa
Kwankwaso ba shi da kudi bai taba satar kudin gwamnati ba yafi kowa farin jini a 2023 – Buba Galadima
Jigo a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Buba Galadima, ya ce, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso, shi ne dan takarar shugaban kasa mafi farin jini kafin zaben 2023.
Da ya ke magana a shirin safe na Arise News, Galadima, ya ce, duk da cewa Kwankwaso ba shi da kudi domin bai taba satar kudin gwamnati ba, amma shi ne dan takarar da zai doke kowa a zaben 2023.
A cewar Galadima: “Dabararmu ita ce za mu nunawa ‘yan Najeriya cewa, dan takara mafi farin jini idan zabe ya gudana shi ne Kwankwaso.
“Kwankwaso ba shi da kudin da zai yi yakin neman zaben shugaban kasa saboda bai saci dukiyar jama’a ba.
“Kowa a fadin duniya ya san cewa Kwankwaso ne dan takarar da ya fi farin jini, Kwankwaso ya na da sihirin da zai magance matsalolin ‘yan Najeriya.”
Ya kuma caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari kan karramawar da aka yi wa ‘yan Najeriya. In ji Dailiy Post.
Galadima ya ce, ya kamata a ce yawancin wadanda aka karrama sun kasance a gidan yari.
Ya kara da cewa “Mutane 440 da Buhari ya ba lambar yabo ta kasa su kasance a gidan yari, a bayar da wadannan kyaututtukan ga mutanen da suka yi ritaya ba tare da wata aibu ba.”
Hangen Dala
Lauyoyin gwamnatin Kano sun bukaci a kamo Ganduje
Babbar kotun jaha mai lamba 7 karkashin jagorancin mai sharia Amina Adamu ta sanya karfe biyu da rabi na ranar yau dan bayyana matsayarta akan batun gurfanar da tsohon gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa da wasu mutane.
A zaman kotun na yau lauyoyin gwamnatin jaha sun bayyana wa kotun cewa an sadar da sammace ga wadanda ake kara ta hanyar kafafen yada labarai kamar yadda kotun ta yi umarni tun a baya amma wadanda ake kara basu samu damar halartar kotun ba dan haka ya roki ko dai a kamo su ko kuma kotun ta ci gaba duk da cewar basa gaban kotun.
Sai dai lauyan wanda ake kara na 6 barrister Nuraini Jimo SAN ya yi suka inda ya bayyana cewar kotun ta dakata tun da sun daukaka kara ya kuma bayyana cewar kotun bata da hurumi sannan kunshin tuhume-tuhumen yana dauke ta kura-kurai.
Kotun zata bayyana matsayarta a yau da rana.
Tun da farko gwamnatin kano ta yi karar Ganduje da mutane 6 bisa zargin almundahana akan kudi sama da Naira Biliyan 4 da aka yi zargin sun sayarda wasu filaye sun raba kudin.
Labarai
Da Dumi Dumi:- EL Rufai ya kai karar majalisar dokoki
Tsohon Gwamna jahar Kaduna Mal. Nasir elrufai ya Maka majalisar Dokokin jahar Kaduna a gaban Kotu a bisa bata Masa Suna da majalisar tayi na cewa Gwamnatin sa ta sace kudaden jahar da Suka naura naira miliyan dubu Dari Hudu.
Tsohon Gwamna ya shigar da karar ce, a Gaban babbar kotun taraiyya dake NDA Kaduna a safiyar Laraban nan 26 ga watan Yuni 2024.
Inda ya bukaci Kotun data tursasa majalisar ta bashi hakuri a bainar jama’a, sakamakon Kazafin da Yan majalisan Suka yi masa da mukarraban Gwamnatinsa data gabata.
Karin bayani na nan tafe….
Siyasa
Zauren jam’iyyun haɗin kan kasa IPAC sun cire shugaban jam’iyyar LP na Kano Abdullahi Raji daga cikin tafiyar su
Sakataren zauren jam’iyyun haɗin kan kasar nan, IPAC na ƙasa reshen jihar Kano, kuma shugaban jam’iyyar APM na Kano Honarable Nuhu Idris, ya ce sun cire shugaban jam’iyyar LP na jihar Kano Abdullahi Raji daga cikin tafiyar su ta IPAC, baki ɗaya.
Sakataren na IPAC, Nuhu Idris ya ce sun dauki wannan mataki ne bisa yadda Rajin ke amfani da kungiyar CUPP, da rusassun jam’iyyun kasar nan suka samar a baya, a dan haka, duk wata jam’iyyar dake da rijista a yanzu na ƙarƙashin IPAC.
Ya kuma ce dokar da ta kafa IPAC, ba ta bai wa ɗan kowacce jam’iyya damar shiga hurumin wata jam’iyyar ba kamar yadda Rajin ke ƙoƙarin yi a rikicin dake faruwa a jam’iyyar APC a nan jihar Kano.
Shugaban jam’iyyar APM, ɗin Honarable Nuhu Idris, ya ce sun cire Rajin daga tafiyar ta IPAC ne, sakamakon wata sanarwa da ya fitar, ya ce, ka da hukumar zaɓe INEC, ta yi watsi da shugaban mazaɓar Ganduje, wanda hakan ba dai-dai ba ne a dokance, dan haka, suka fitar da shi daga cikin tafiyar tare da sanar da shugabancin jam’iyyar sa na kasa.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su