Connect with us

Labarai

Magidanci ya lakadawa jaririya duka har an yanke hannunta wai ta hana shi bacci

Published

on

Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa NHRC da kungiyar mata ‘yan jarida ta Najeriya NAWOJ sun yi Allah wadai da cin zarafin wani jariri a jihar Imo.

Sun kuma tuhumi gwamnatin Imo da hukumar ‘yan sandan Najeriya da su gaggauta kama mai laifin, Confidence Amatobi tare da gurfanar da shi gaban kuliya.

Ana zargin mahaifin wanda dan asalin Amurie ne a karamar hukumar Isu da laifin yiwa jaririyarsa mai suna Miracle dan watanni 2.

Rahotanni sun ce, Amatobi mai shekaru 31 da haihuwa ya lakada wa jaririya duka da rataya mai roba tare da karya hannun jaririn saboda ya dagula masa barci.

Wannan tashin hankalin ya kai ga yanke sassan jikin da ya karye a cibiyar kula da lafiya ta tarayya (FMC) da ke Owerri.

Shugabar kungiyar ta NAWOJ, Dorothy Nnaji, wacce ta yi magana da manema labarai bayan ta ziyarci Miracle, ta ce Amatobi ya yi ta bugun yaron har ya hana shi kuka.

“Wanda ya aikata laifin, Confidence Amatobi, ya yi amfani da rataya mai filastik a kan jariririyar, kawai saboda kukan da uwar ta tafi domin ta samu sauki.

“Ya yi amfani da itace da igiya na roba don ɗaure hannun jariririyar lokacin da ya ga hannun ya karye kuma ya kumbura,” in ji ta.

Ya kulle uwa da yaron domin hana ta neman taimako daga makwabta.

“Hannun jaririn ya riga ya ruɓe. Hanya daya tilo ita ce a yanke hannun dama na Miracle daga kafada,” in ji ta.

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Trending