Connect with us

Wasanni

Ronaldo na gab da komawa gida daga Mancehster United

Published

on

Dan wasan gaba na Manchester United, Cristiano Ronaldo na shirin komawa Sporting Lisbon, kungiyar da ta ke buga gasar cin kofin zakarun Turai nan gaba kadan.

Mai horas da Sporting Lisbon, Ruben Amorim, ya bayyana cewa, kungiyar ta Portugal ta na ‘mafarkin’ daukar Ronaldo daga Manchester United.

Ronaldo ya yi atisaye da kungiyar Man United ta farko a karon farko a ranar Talata tun bayan da ya ki zuwa a makare a wasan da suka doke Tottenham da ci 2-0 a makon jiya.

Wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar, wanda ke da muradin barin Old Trafford a bazara, kocin Manchester United Erik ten Hag ya kore shi saboda rashin biyayya da ya yi, kuma aka bar shi cikin ‘yan wasan da suka tashi kunnen doki 1-1 da Chelsea a karshe. karshen mako.

An danganta dan wasan mai shekaru 37 da barin Man United lokacin da aka sake bude kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa a watan Janairu, inda Chelsea ke zawarcinsa.

Sai dai kuma an fara tunanin komawa Sporting Lisbon, inda Ronaldo ya fara taka leda.

Duk da haka, Amorim yanzu ya yarda cewa Sporting Lisbon ba ta da kuɗin biyan albashin Ronaldo saboda dole ne kyaftin din Portugal ya rage albashi mai yawa don shiga tsohuwar kungiyarsa.

“Ronaldo babban dan wasa ne,” in ji Amorim a taron manema labarai kafin wasan da Sporting Lisbon za ta yi da Tottenham a gasar zakarun Turai ranar Laraba.

“Dan wasan Manchester United ne. Kowa a Sporting yana mafarkin dawowar Cristiano, amma ba mu da kuɗin da za mu biya albashinsa.

“Ina tsammanin ya na farin ciki a Manchester amma ba ya wasa, don haka shine matsalar.

“Amma ina da matsaloli na, don haka matsalar Ten Hag ce! Ina matukar farin ciki da ‘yan wasa na, ba matsala ko kadan a halin yanzu.”

Ronaldo ya shafe shekaru biyar a Sporting Lisbon tsakanin 1997 zuwa 2002.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending