Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Muna sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a Twitter – Gwamnati

Published

on

Gwamnatin tarayya, ta ce, a halin yanzu tana sa ido kan al’amuran a shafin Twitter bayan saye kamfanin da Elon Musk ya yi.

Lai Mohammed, ministan yada labarai da al’adu ne ya bayyana hakan, a jawabin bude taro karo na uku na shirin ‘PMB Administration Scorecard 2015-2023’.

An kaddamar da shirin ne a watan da ya gabata, domin nuna nasarorin da gwamnatin shugaba Buhari ta samu.

Ya kuma yi bayani ne akan nasarorin da Buhari ya samu a harkar sufurin jiragen sama.

Ya kara da cewa, akwai tambayoyi game da me zai kasance a yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta kulla da Twitter, ganin yadda aka samu sauyin mallakarsa.

“Mutane da yawa sun nemi a mayar da martani bayan rahotannin da ke cewa, an samu karuwar labaran karya, rashin fahimta da kuma kalaman nuna kiyayya, tun lokacin da shafin ya sauya ikon mallakar,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai ranar Alhamis.

“Da yawa ma sun tambaye mu ko wani haramcin yana kan aiki. Bari in faɗi haka: Muna sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a Twitter.

“Ba mu taba nufin mu haramta duk wani dandalin sada zumunta ba ko kuma murkushe ‘yancin fadin albarkacin baki. Ba komai.

“Abin da ya faru a shafin Twitter sananne ne ga kowa. Twitter ya zama dandalin zabi ga masu son tada zaune tsaye a Najeriya ta hanyar yin amfani da labaran karya, yada labarai da kalaman kiyayya.

“Babu wata al’umma da za ta bari duk wani dandalin sada zumunta ya jefa shi cikin rudani. Tabbas ba Najeriya ba. Amma mun ci gaba da yin aiki mai kyau tare da shafin daban-daban na kafofin yada labarai, ciki har da Facebook, Google (masu mallakin YouTube) da Twitter.

“Ba mu da niyyar sake haramta duk wani dandalin sada zumunta. Amma kuma ba za mu zauna mu kyale duk wani dandali da zai jefa al’ummarmu cikin mawuyacin hali ba.”

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon

Published

on

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar

Published

on

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.

Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.

Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.

Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar

Published

on

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Karin bayani nan tafe….

Continue Reading

Trending