Connect with us

Wasanni

Qatar 2022: Duk da rauni Belgium ta sa Lukaku a tawagar ta

Published

on

An saka Romelu Lukaku a cikin ‘yan wasa 26 da Belgium za ta wakilci kasar a gasar cin kofin duniya ta Qatar, duk da raunin da ya ji.

Babban koci Roberto Martinez ya yi gargadin cewa dole ne Lukaku ya nuna koshin lafiyarsa a matakin rukuni idan har ana so a saka shi a cikin tawagar, wanda da alama dan wasan ya yi.

Dan wasan da ya kafa tarihi a Belgium, Lukaku, wanda aro a Inter daga Chelsea, ya dawo daga jinyar raunin da ya samu, inda ya fito daga benci inda ya zura kwallo a ragar Viktoria Plzen a gasar cin kofin zakarun Turai ranar 26 ga watan Oktoba.

Duk da haka, wannan shine daya daga cikin wasanni biyu kacal da dan wasan mai shekaru 29 ya gudanar tun watan Agusta, inda wasansa na karshe ya kasance ranar 29 ga Oktoba da Sampdoria.

A ranar 23 ga watan Nuwamba ne Belgium za ta fara gasarta da Canada, kafin ta kara da Morocco da Croatia a sauran wasanninsu na rukunin F.

Tawagar Belgium: Koen Casteels (Wolfsburg), Thibaut Courtois (Real Madrid), Simon Mignolet (Club Brugge); Toby Alderweireld (Royal Antwerp), Timothy Castagne (Leicester City), Zeno Debast (Anderlecht), Leander Dendoncker (Aston Villa), Wout Faes (Leicester City), Thomas Meunier (Borussia Dortmund), Arthur Theate (Rennes), Jan Vertonghen ( Anderlecht); Yannick Carrasco (Atletico Madrid), Kevin De Bruyne (Manchester City), Thorgan Hazard (Borussia Dortmund), Amadou Onana (Everton), Youri Tielemans (Leicester City), Hans Vanaken (Club Brugge), Axel Witsel (Borussia Dortmund); Michy Batshuayi (Fenerbahce), Charles De Ketelaere (Milan), Jeremy Doku (Rennes), Eden Hazard (Real Madrid), Romelu Lukaku (Inter), Dries Mertens (Galatasaray), Lois Openda (Lens), Leandro Trossard (Brighton and Hove). Albion)

Labarai

Real Madrid ta kaddamar da Alexander

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta ƙaddamar da ɗan wasa Trent Alexander Arnold a yau a matsayin ɗan wasan ta

Inda shugaban ƙungiyar Flerontino Perez yace yau suna matuƙar Farin ciki kasancewar sun mallaki babban ɗan wasan baya a duniya.

 

Shima ɗan Wasa Arnold ya bayyana cewa yana cikin farin ciki kuma mafarkin sa ya cika na zama ɗan Wasan Madrid a yau.

Continue Reading

Labarai

Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Published

on

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.

A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Continue Reading

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Trending