Connect with us

Wasanni

Qatar 2022: Kimar Brazil ta ragu a idon duniya – Roberto Carlos

Published

on

Tsohon dan wasan baya na Real Madrid, Roberto Carlos, ya yi imanin cewa kungiyar kwallon kafa ta Brazil ba kamar yadda ta ke a da ba.

A cewar Carlos, Brazil ba ta nuna farin ciki irin na kwallon kafa kamar yadda ta saba yi a zamaninsa, ya kara da cewa, ‘yan wasan na yanzu sun rasa jigon sa.

Tsohon dan wasan baya na hagu ya taka leda a gasar cin kofin duniya hudu a karkashin manajoji da salo iri-iri.

Da ya ke magana da jaridar Telegraph gabanin bude gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022 da Brazil za ta yi da Serbia a ranar Alhamis, 24, Carlos ya ce, “Brazil ta rasa ainihin ta, kyakkyawan wasan.”

“Mun kai hari a matsayin kungiya, amma kuma mun kare sosai fiye da yanzu. Mun kasance da kwarin gwiwa a wasanmu na matsayi.”

Brazil ta na rukunin G a gasar cin kofin duniya ta 2022, kuma za ta kara da Serbia, Switzerland da Kamaru.

Wasanni

Dembele ya tallafawa Barcelona ta kai wasan kusa da na karshe

Published

on

Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Ousmane Dembele ne, ya zurawa Barcelona kwallo daya tilo a wasan kusa da na karshe da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta Real Sociedad, a gasar Copa Del Rey da ke gudana a kasar ta Spain, wanda hakan ne yabawa Barcelona damar zuwa wasan kusa da na karshe a gasar.

Kawo yanzu, dan wasa Ousmane Dembele ya zurawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona kwallaye bakwai a kakar wasannin nan da muke ciki.

Continue Reading

Wasanni

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta dauki aron Danjuma daga Villarreal

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta sanar da daukan aron dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Villarreal dan asalin kasar Netherlands wato Arnaut Danjuma mai shekaru 25 har zuwa karshen kakar nan da muke ciki.

Tun bayan da aka bude kasauwar saye da sayarwa na ‘yan wasanni a watan janairun nan da muke ciki, Arnaut Danjuma, shine dan wasa na farko da Tottenham Hotspur din ta dauka.

Tottenham Hotspur ta na mataki na biyar a teburin gasar firimiyar kasar Ingila ta shekarar 2022 zuwa 2023 da muke ciki.

Continue Reading

Wasanni

Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta kori Lampard

Published

on

Tsohon da wasan kasar Ingila mai shekaru 44 Lampard ya karbi aikin horas da kungiyar kwallon kafa ta Everton a watan janairun shekarar 2022 da ta gaba ta, bayan sallamar mai horas da ita na wancan lokacin Rafael Benitez.

Everton dai ta yi rashin nasara a wasanni tara cikin wasanni 12 da ta buga a gasar Firimiyar kasar Ingila ta shekarar 2022 zuwa 2023 da muke ciki.

A ranar Asabar din da ta gabata dai kungiyar kwallon kafa ta Everton ta yi rashin nasara a karawar da ta yi da kungiyar kwallon kafa ta West Ham United, wanda hakan yasa ta ke mataki na 19 da maki 15 a teburin gasar ta bana.

Continue Reading

Trending