Connect with us

Labarai

An kusa kammala aikin ginin gidan gyaran halin Jan Guza – Ra’uf Aregbesola

Published

on

Gwamantin tarayya ta ce, nan bada daɗewa ba za a kammala aikin ginin gidan gyaran hali da ke garin garin Jan Guwa a jihar Kano.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Ra’uf Aregbesola a harabar gidan gyaran halin na Jan Guza a wata ziyarar duba aikin da ya kawo a ranar Asabar.

Yana mai cewa, ya gamsu da yadda ake yin aikin duba da yadda ake yin sa mai ingancin gaske.

Sabon gidan gyaran halin dai na Jan Guza ya kunshe abubuwa daban-daban da suka haɗar da tarin ɗakunan ɗaurarru da wajan koyon sana’o’in su da kotuna da dai sauran su.

Yayin ziyarar aikin, yana tare da rakiyar shugaban hukumar gidan gyaran halin na ƙasa da na jihar Kano, sai kuma shugaban hukumar Civil Defence na ƙasa da kuma na hukumar kula da shige da fice shima da sauran manyan ofisoshin su.

Labarai

Matsin Rayuwa: Mun fitar da tsarin baiwa daliban mu aiki a lokacin karatun su domin taimaka musu – Jami’ar Bayero

Published

on

Jami’ar Bayero dake jihar Kano ta ce halin matsin rayuwar da al’umma suka samu kansu yanzu a ciki, ya sa yanzu haka suka fito da tsarin baiwa daliban makarantar aiki a lokacin da suke tsaka da karatun su a jami’ar, domin saukaka wa karatun daliban.

Shugaban jami’ar Farfesa Sagir Ahmad Abbas, ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala FM, a yau Litinin, a wani bangare na shirin bikin yaye daliban jami’ar su 11,000, karo na 38, da za’a fara daga gobe Talata, ya kuma ce ta hanyar taimakawar ne daliban za su kai ga gaci a karatun su.

Da yake nasa jawabin mai taimakawa shugaban jami’ar Bayeron dake Kano, akan harkokin gudanarwa Farfesa Umar Sani, shawartar dalibai ya yi da su kara jajircewa tare da mayar da hankali akan karatun su, ta yadda zasu samu nasara da kuma cin ma gaci.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawairto cewa shuganan Jami’ar Bayeron dake Kano Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya kuma ce za su gudanar da bikin yaye daliban jami’ar ne a kwanaki hudu ko biyar, domin baiwa dalibai, da iyaye da ma malamai damar gudanar da bikin yadda ya kamata sabanin a baya da kwanakin basu kai haka ba.

Continue Reading

Ilimi

Za’a daga likafar BMC zuwa Diploma – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin Kano tace nan bada jimawa ba za’a daga likafar makarantar koyon aikin jarida a matakin farko wato BMC ta Goron Dutse zuwa tsarin Diploma.

Mataimakin gwamnan Kano Kwamred Aminu Abdussalam ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake jawabi a wurin taron da kungiyar tsaffin daliban makarantar suka shirya.

Kwamred Aminu Abdussalam ya kuma ce nan bada jimawa ba makarantar za’a daga matsayin karatun daga Certificate zuwa Diploma, kamar yadda makarantar ta bukata.

Kazalika yace gwamnatin Kano za ta cigaba da lura da dukkanin kayan koyo da koyarwa har ma da ababen hawa na hukumar ilimin manya ta Kano, wato Agency for mass Education wadda a cikin ta ake karatun na jarida.

Taron dai wanda shi ne karo na farko da gamayyar kungiyar daliban ta shirya tun bayan kafuwar makarantar shekaru 38 da ta gabata, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da suka haɗar da Kwamishinan ilimi na Kano da Kwamishinan yada labarai da kwamishiniyar mata da mai baiwa gqamna shawara kan harkokin yada labarai.

Kazalika taron ya samu halartar Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da tsaffin malaman makarantar da kuma shugabannin kafafen yada labarai na Kano.

A yayin taron dai shugaban kungiyar taaffin daliban Ismaila Ammai me Zare ya kaddamar da wani tsari na tallafawa makarantar da abin zama mai taken ( ka dawo da kujerar ka ).

Continue Reading

Labarai

Tsaftar Muhalli: Ba zamu lamunci fitowar kwallon kafar da matasa suke yi duk karshen wata ba a Kano – Ma’aikatar Muhalli

Published

on

Ma’aikatar muhalli ta jihar Kano ta ce, ba za ta lamunci halayyar da wasu matasa suke nunawa a kowanne karshen wata na yin kwallon kafa a kan tituna ba.

Kwamishinan muhalli na jihar Kano Nasiru Sule Garo, ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala duban tsaftar muhalli na karshen wata yau a ƙwaryar birnin Kano.

Garo ya ce, yanayin da mutane suka nuna na rashin biyayya ga dokar tsaftar muhalli abin takaici ne matukar gaske, inda ya ce kuma ba za su lamunci hakan ba.

Nasir Sule Garo ya kuma ce, za a gayyaci mahukuntan kasuwar Abbatuwa domin tattaunawa da su kan yin biyayya ga dokar tsaftar muhallin.

Wakiliyarmu Madina Shehu Hausawa ta rawaito cewa, kotun tafi da gidanka mai kula da tsaftar muhalli ƙarƙashin mai Shari’a Auwal Yusuf Sulaiman ta yanke hukuncin tara nan take ga wadanda suka karya doka a yau Asabar.

Continue Reading

Trending