Connect with us

Siyasa

Jigawa za ta baiwa Tinubu ruwan kuri’u – Badaru

Published

on

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya yi alkawarin baiwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC, dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu kuri’u dari a zaben 2023 mai zuwa.

Gwamna Badaru ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a wajen kaddamar da yakin neman zaben fidda gwanin takarar gwamna na jam’iyyar APC ta Arewa maso Gabas da aka gudanar a Hadejia.

Badaru ya bayyana cewa an yi bikin ne domin gabatar da jama’a, dan takarar gwamna, ‘yan takarar Sanata, da sauran ‘yan takara daga shiyyar.

Da ya ke jawabi ga dimbin jama’a, Gwamna Badaru, ya ce Bola Tinubu ne dan takarar shugaban kasa daya tilo da zai iya ceto kasar nan daga halin kuncin tattalin arziki da kuma kokarin ci gaban kasar.

“Duba tarihinsa da gogewarsa, na tabbata yana da tsare-tsare da manufofin da za su taimaka wajen ci gaban kasa,” in ji shi.

Ya bayyana cewa taron jama’ar da suka taru ya nuna karara ga jam’iyyun adawa cewa Jigawa ta APC ce kuma a shirye take ta ci gaba da rike madafun iko a zaben 2023 mai zuwa.

Siyasa

Rurum ya sanar da ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC a zauren Majalisar Wakilai

Published

on

Shugaban majalisar Wakilai ta Ƙasa Tajudden Abbas, ya karanta takardar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure, RT. Honarable Kabiru Alhassan Rurum, ta ficewarsa daga Jam’iyyar NNPP zuwa Jam’iyyar APC, a hukumance.

Tajuddeen Abbas, ya karanta takardar sauyin sheƙar da Rurum din yayi a harabar Majalisar, a zamanta na yau Alhamis.

Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai bai wa Rurum, shawara na musamman akan shafukan sada zumunta Fatihu Yusuf Bichi, ya fitar a ranar Alhamis 15-05-2025.

Tun dai a baya an jiyo yadda Honarable Kabiru Alhassan Rurum, ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, wanda a yanzu na tabbatar da ficewar tasa a hukumance a zauren Majalisar Wakilai ta ƙasa.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau shugaban kasa zai dawo daga Faransa

Published

on

Bayan ziyarar aiki ta kusan mako biyu Zuwa kasar Faransa a yau litinin ake saka ran shugaban kasa zai dawo gida Nigeria.

Cikin sanarwar da hadimin shugaban kasar kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar ya ce kowa ne lokaci daga yanzu shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu zai sauka a Nigeria domin cigaban da harkokin mulkin kasar.

Continue Reading

Hangen Dala

Kofar APC a bude take ga masu shiga – Abdullahi Abbas

Published

on

Jamiyyar APC a Jihar Kano tace Kofar ta a bude take ga dukkanin masu son shigowa jamiyyar.

 

Shugaban jamiyyar na Kano Hon Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.

 

Abbas yace labarin dake yawo cewa akwai wadanda ke Shirin shigowa jamiyyar, su sani Kofar APCn a bude take tare da maraba ga dukkanin wadanda zasu shigo.

 

Koda dai Abdullahi Abbas yace shigowa APC ba zai hana tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa ba, koma kaucewa hukumar EFCC da ICPC.

 

A baya bayan nan ne dai aka rinka yada cewa mabiya jamiyyar NNPP kwankwasiyya na Shirin shiga jamiyyar APC tare da madugun ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Continue Reading

Trending