Connect with us

Siyasa

Rikicin PDP: Da sauran Rina a Kaba har yanzu

Published

on

Alamu sun nuna cewa rikicin cikin gida da ake fama da su a cikin jam’iyyar PDP har yanzu ba su kau ba a tsakanin gwamnonin G5.

Hakan ya biyo bayan gayyatar da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi wa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, LP, na kaddamar da daya daga cikin ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar a jihar.

Dr Yunusa Tanko, kakakin yakin neman zaben shugaban kasa Obi/Datti ne ya bayyana hakan.

Ku tuna cewa Gwamna Wike ba sabon abu bane wajen gayyatar mambobin jam’iyyar adawa, musamman daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), zuwa bude ayyukan sa jihar sa.

A watan Agustan bana ne gwamnan ya gayyaci gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, dan jam’iyyar APC, domin kaddamar da aikin gadar sama, a fitaccen mahadar Waterlines dake kan titin Aba, lamarin da ya haifar da rade-radin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki da kuma shirye shiryen da ya dauka. domin yiwa Bola Ahmed Tinubu aiki dan takarar APC.

Wike, wanda a halin yanzu yake jagorantar kungiyar gwamnonin G5 da ke da Samuel Ortom na jihar Benue, Seyi Makinde na jihar Oyo, Okezie Ikpeazu na jihar Abia, Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu a matsayin mambobi, kwanan nan ya nuna cewa kungiyarsa na iya kokarin sasantawa da dan takarar shugaban kasa. na PDP, Atiku Abubakar, bayan shafe watanni ana tafka muhawara.

Da ya ke raba gayyatar a shafinsa na Twitter, Tanko ya rubuta cewa, “Muna gab da kwato Najeriya ga al’ummar Najeriya….. Ku biyo mu mutanen Jihar Ribas!!!. Muna ci gaba da motsi cikin ƙoshin lafiya.”

Siyasa

Rurum ya sanar da ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC a zauren Majalisar Wakilai

Published

on

Shugaban majalisar Wakilai ta Ƙasa Tajudden Abbas, ya karanta takardar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure, RT. Honarable Kabiru Alhassan Rurum, ta ficewarsa daga Jam’iyyar NNPP zuwa Jam’iyyar APC, a hukumance.

Tajuddeen Abbas, ya karanta takardar sauyin sheƙar da Rurum din yayi a harabar Majalisar, a zamanta na yau Alhamis.

Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai bai wa Rurum, shawara na musamman akan shafukan sada zumunta Fatihu Yusuf Bichi, ya fitar a ranar Alhamis 15-05-2025.

Tun dai a baya an jiyo yadda Honarable Kabiru Alhassan Rurum, ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, wanda a yanzu na tabbatar da ficewar tasa a hukumance a zauren Majalisar Wakilai ta ƙasa.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau shugaban kasa zai dawo daga Faransa

Published

on

Bayan ziyarar aiki ta kusan mako biyu Zuwa kasar Faransa a yau litinin ake saka ran shugaban kasa zai dawo gida Nigeria.

Cikin sanarwar da hadimin shugaban kasar kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar ya ce kowa ne lokaci daga yanzu shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu zai sauka a Nigeria domin cigaban da harkokin mulkin kasar.

Continue Reading

Hangen Dala

Kofar APC a bude take ga masu shiga – Abdullahi Abbas

Published

on

Jamiyyar APC a Jihar Kano tace Kofar ta a bude take ga dukkanin masu son shigowa jamiyyar.

 

Shugaban jamiyyar na Kano Hon Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.

 

Abbas yace labarin dake yawo cewa akwai wadanda ke Shirin shigowa jamiyyar, su sani Kofar APCn a bude take tare da maraba ga dukkanin wadanda zasu shigo.

 

Koda dai Abdullahi Abbas yace shigowa APC ba zai hana tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa ba, koma kaucewa hukumar EFCC da ICPC.

 

A baya bayan nan ne dai aka rinka yada cewa mabiya jamiyyar NNPP kwankwasiyya na Shirin shiga jamiyyar APC tare da madugun ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Continue Reading

Trending