Connect with us

Wasanni

‘Yan wasan Super Eagles sun sauka a sansanin su na Lisbon

Published

on

‘Yan wasa 11 ne suka isa sansanin Super Eagles da ke Lisbon, gabanin wasan sada zumuncin kasa da kasa da za su fafata  da Portugal.

Mataimakin kyaftin, William Troost-Ekong, Alex Iwobi, Joe Aribo da Ademola Lookman ne suka fara sauka a sansanin.

Sauran ‘yan wasan da ke sansanin su ne Bruno Onyemaechi da Kevin Akpoguma da Oghenekaro Etebo da Ebube Duru da Emmanuel Dennis Paul Onuachu da kuma Calvin Bassey.

A na sa ran sauran ‘yan wasan 12 za su shiga cikin takwarorinsu a ranar Talata.

Tuni dai babban mai horaswa, Jose Peseiro ya gayyaci Cyriel Dessers da Chidozie Awaziem a matsayin wadanda za su maye gurbin Victor Osimhen da Olisa Ndah.

Kungiyar za ta yi atisayen farko a daren yau.

Za a yi wasan ne da karfe 8 na dare agogon Najeriya.

Labarai

Real Madrid ta kaddamar da Alexander

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta ƙaddamar da ɗan wasa Trent Alexander Arnold a yau a matsayin ɗan wasan ta

Inda shugaban ƙungiyar Flerontino Perez yace yau suna matuƙar Farin ciki kasancewar sun mallaki babban ɗan wasan baya a duniya.

 

Shima ɗan Wasa Arnold ya bayyana cewa yana cikin farin ciki kuma mafarkin sa ya cika na zama ɗan Wasan Madrid a yau.

Continue Reading

Labarai

Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Published

on

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.

A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Continue Reading

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Trending