Connect with us

Siyasa

Rikicin cikin PDP: Zan tallafawa da Obi kayan aiki a zaben 2023 – Wike

Published

on

Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers a ranar Alhamis ya yi alkawarin tallafawa Peter Obi, , dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party, LP.

Wike ya ce zai bada tallafin kayan aiki a lokacin yakin neman zaben Obi a jihar Ribas.

Ya yi alkawarin baiwa Obi goyon baya a lokacin da ya furta hakan a wurin bikin kaddamar da gadar sama ta Nkpolu-Oroworokwo a Fatakwal.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, Obi ya na da abin da ake bukata domin zama shugaban Najeriya.

A cewar Wike: “Duk lokacin da kuke son yin yakin neman zabe a jihar, ku sanar da ni, duk tallafin dabaru, za mu ba ku.”

Obi, da abokin takararsa, Datti Baba-Ahmed, da wasu mambobin kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na LP, sun je Rivers domin kaddamar da gadar sama ta 9 da gwamnatin Wike ta yi.

A cikin ‘yan watannin da suka gabata, Wike ya na mu’amala da jiga-jigan wasu jam’iyyun siyasa.

Wannan mataki na Wike dai na iya kasancewa ga korafe-korafen sa da shugabancin jam’iyyar PDP, biyo bayan kayen da ya sha a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.

Manyan Labarai

Jam’iyyar PDP ta dakatar da Ayu

Published

on

Kwamitin zartarwar jam’iyyar PDP na karamar hukumar Boko a jihar Benue ya dakatar da shugaban ta na kasa Sanata Iyochia Ayu daga jam’iyyar.

Yayin yanke hukuncin sakataren jam’iyyar na karamar hukumar ta Gboko Banga Dooyum yace sun dakatar da Ayu ne sakamakon zargin sa marawa wata jam’iyya baya wato anti party.

Kazalika dakatarwar za ta fara aiki ne nan take, sakamakon yadda kwamitin yace bashi da kwarin gwiwar Kan cigaba da jagorancin sa a jam’iyyar PDP.

Continue Reading

Manyan Labarai

Atiku ya fasa zuwa jihar Rivers

Published

on

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya soke ziyarar neman kuri’a da zai Kai Jihar Rivers.

Cikin wata sanarwa da Atikun ya fitar ya bayyana cewa rashin ingataccen tsaro shi ne musabbabin soke ziyarar.

Idan zaa iya tunawa dai akwai jikakkiya tsakanin Dan takarar Atiku Abubakar da Kuma gwamnan jihar ta Rivers Nyeson Wike, wanda Wiken ya lashi takobin kayar da jam’iyyar ta PDP a matakin takarar shugabancin kasa.

 

Continue Reading

Manyan Labarai

Kano ta tsakiya= Abinda yasa har yanzu INEC ba ta sauya sunan Shekarau da Rufa’i Hanga ba – NNPP

Published

on

Jam`iyyar NNPP, ta nuna damuwa game da kin amincewar da hukumar zabe ta yi da wasu sunayen da ta gabatar mata domin maye gurbin wasu daga cikin `yan takararta da suka janye.

Jam`iyyar ta ce ta kai maganar gaban alkali, kuma sau biyu kotu tana ba ta gaskiya, amma hukumar zaben ta ci gaba da yin turjiya.

NNPP, ta ce ta bi dukkan ka’idojin da doka da INEC ta shimfida wajen mika sunayen ‘yan takararta na mukamai daban-daban ciki har da kujerar sanatan Kano ta tsakiya, wadda tsohon gwamnan jihar sanata Ibrahim Shekarau, ya janye bayan ficewarsa daga jam’iyyar.

To amma, jam’iyyar ta fara zargin hukumar zabe nayi mata wasa da hankali har ma ta fara zargin ko akwai wata rufa-rufa da hukumar zaben keyi mata.

Injiniya Buba Galadima, jigo ne a jam’iyyar ta NNPP, ya shaida wa BBC cewa, su babban abin da ya dame su shi ne ko akwai wata jikakkiya tsakaninsu da hukumar zabe wadda ba su sani ba.

Ya ce, “ Duk dan Najeriya ya sani cewa Malam Ibrahim Shekarau, ya bar jam’iyyar NNPP, mun rubuta wa INEC cewa tun da Shekarau ya bar mu a bamu ranar da zamu sake zaben fitar da wani dan takarar da zai maye gurbin Shekarau.”

To amma sai INEC, ta rubuto cewa bata yarda ba, mu kuma muka fitar da dan takara muka aika musu amma suka ce ba su yarda ba,” inji shi.

Buba Galadima, ya ce daga nan suka garzaya zuwa kotu, kotu kuwa ta ce suna da gaskiya.

Ya ce, “Daga nan ne sai INEC, ta ce bata yarda ba ta daukaka kara, kotu ta gaba kuwa ta ce dole a kyale jam’iyyar da ya bari ta fitar da wani dan takara, sai suka ce sai sun sake daukaka kara zuwa kotun koli.”

Buba Galadima, ya ce ‘’ Wai shin mene ne ma bukatar INEC?”.

Bayan kujerar dan takarar sanata ta Kano ta tsakiya, akwai wasu kujerun kamar ta dan takarar sanata a jam’iyyar a Taraba ta Kudu Murtala Garba, wadanda a har yanzu hukumar zabe bata karbesu ba.

To sai dai kuma hukumar zaben ta ce bata da wata manufa game da jinkirin da ta ke yi wajen karbar sunayen masu takarar, face bukatar abi doka.

Wani babban lauyan a hukumar zaben, Tanimu Muhammad, ya shaida wa BBC cewa, ita hukumar zabe babu abin da take bukata illa kawai abi doka.

Ya ce,’’ Jam’iyyar NNPP ce ta fara gurfanar da mu gaban kotu, kuma ita kara a kan batun zabe karace da zata iya zuwa har kotun koli, shi ya sa muka tafi can don muna son sanin abin da ya kawo rikici tsakaninmu da ‘ya’yan jam’iyyar.”

Babban lauyan ya ce abin da suke nema su yi ya sabawa jadawalin da muka bayar.

Baya ga jam’iyyar NNPP, akwai wasu jam’iyyun da dama wadanda ke da irin wadannan korafi ko bukatar sauya sunayen da suke so su maye gurbin wasu ‘yan takara da suka janye, da suma suka zuba ido don ganin yadda zata kaya tsakanin hukumar zaben ta kasa da kuma jam’iyyar NNPP.

Continue Reading

Trending