Connect with us

Labarai

Mun kwato Naira biliyan 117 a cikin watan Janairu zuwa Agusta – Hukumar Yaki da Rashawa

Published

on

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC), Farfesa Bolaji Owasanoye, SAN, OFR, ya bayyana cewa, hukumar ta kwato sama da Naira biliyan 117 tsakanin watan Janairu zuwa Agusta 2022.

Farfesa Owasanoye ya bayyana hakan ne a gaban kwamitin majalisar wakilai kan yaki da cin hanci da rashawa a lokacin da hukumar ke kare kudirin kasafin kudin 2023 a Abuja.

Yayin da yake magana kan kasafin kudin shekarar 2022, shugaban ya bayar da takaitaccen bayanin kudaden da aka kwato da suka hada da N1.413bn da $225,965 a asusun ajiyar ICPC/TSA da tsabar kudi N1.264bn ta hanyar shiga haraji.

Sauran wuraren da aka kwato sun hada da filaye, gine-gine da aka kammala, motoci, kayan lantarki da kayan ado da kudinsu ya kai Naira miliyan 679.13, Naira biliyan 2.603, Naira miliyan 81.1, Naira miliyan 1.55 da Naira 195,500.

A yayin da yake bayar da gudunmuwarsa a lokacin tsaron kasafin kudin, shugaban kwamitin majalisar wakilai kan yaki da cin hanci da rashawa, Honorabul Nicholas Garba Shehu, ya yaba wa shugaban hukumar ta ICPC da shugabannin hukumarsa bisa yadda suke ba da jagoranci mai nagarta da hangen nesa, inda ya bayyana cewa salon shugabancinsu ya koma kan gaba daya. arzikin hukumar zuwa ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai fafutuka.

Garba ya umarce su da kada su zubar da kwallon amma su ci gaba da tashi sama.

Don haka, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta saki ragowar kasafin kudin hukumar na shekarar 2022 domin samun damar cimma burinta.

Shugaban kwamitin ya kuma bukaci ICPC da ta samar da wata manhaja ta wayar salula da za ta tona asirin ‘yan Najeriya ,domin su yi amfani da ita wajen kai rahoton ayyukan cin hanci da rashawa a duk inda suke.

Labarai

Mu taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi domin rage musu raɗaɗin rayuwa – Ambada Muhammad

Published

on

Shugaban ƙungiyar mu haɗa zumunci ta KHZ Foundation dake nan Kano Ambasada Dakta Muhammad Abdulsalam, ya ce, taimakawa masu ƙaramin ƙarfi musamman a wannan lokaci na watan Azumin Ramadana, zai taimaka musu wajen rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Ambasada Muhammad Abdulsalam ya bayyana hakan ne a yayin taron baiwa iyayen marayu da masu ƙaramin ƙarfi tallafin kayan abinci a ofishin kungiyar yau Litinin, da kuma basu a wasu unguwanni da suka haɗar da Tukuntawa da Sabuwar Gandu, Tinshama da dai sauransu.

Ya kuma ce, kamata yayi al’umma su ƙara himma wajen shiga makamancin ƙungiyar su domin baiwa al’umma gudunmawar da ta kamata, ta hanyoyi daban-daban, domin cire musu wata damuwa da ta damesu a rayuwa.

“Zamu fitar da ɗaurarru masu ƙananan tara a wasu gidjen ajiya da gyaran hali domin fitar da su daga halin rayuwar da suke ciki na jarrabta da suka tsinci kan su”. In ji Ambasada Muhammad.

Da yake nasa jawabin malami a kwalejin ilmin tarayya ta FCE dake nan Kano Mallam Ibrahim Muhammad Gandu, gargaɗar iyayen marayun da sukaci gajiyar tallafin yayi, da su yi amfani da kayayyakin abincin ta hanyar da ta dace Mai-makon siyar da kayan a ƙasƙance da ake zargin wasu suna yi a wasu lokutan.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar, iyayen marayu da masu ƙaramin ƙarfi da dama ne suka rinƙa bayyana farin cikinsu, bisa basu kayan abincin da akayi, wanda suka haɗar da Shinkafa, Gero Taliya Man girki da sai sauransu, haɗi da Naira dubu ɗaya kuɗin Mota ga kowannen su.

Continue Reading

Labarai

Ɗaurarru sama da dubu 1 aka duba lafiyar su a Kano

Published

on

Ɗaurarru sama da dubu ɗaya ne dake zaune a gidajen gyaran hali na goron Dutse da Kurmawa a jihar Kano, suka amfana da ganin likitoci daban-daban tare da ba su magani kyauta.

Yayin wani aikin sa kai da nufin neman lada a wajan Allah da tawagar ƙungiyar likitoci musulmi suka yi, ƙarƙashin jagarancin shugaban kwanitin gudanar da aikin Dr. Sule Abdullahi Gaya.

Har ma shugaban ƙungiyar na jihar Kano, Dr. Muhammad Auwal ya ce, suna yin aikin ne domin taimakawa marasa ƙarfi a wurare daban-daban, tare da basu kayan abinci da ruwa, da makamantan su.

A jawaban su daban-daban Dr. Anas Ibrahim Yahaya Bichi da Dr. Muhammad Lawan Adamu waɗanda suna cikin likitocin da suka duba marasa lafiya da dama cewa suka yi, a tafiyar ta su babu irin likitan da babu, don haka kowacce irin cuta suka ci karo da ita sun tanadi maganin ta.

Daga bisani mai kula da gidan gyaran halin na Kurmawa DC Mu’azu Tukur wanda ya yi jawabi a madadin shugaban hukumar ya nuna godiya da jin dadin su kan aikin da kungiyar likitoci musulmi suka yi ga daurarrun.

Continue Reading

Labarai

Tallafawa masu ƙaramin ƙarfi na rage musu raɗaɗin rayuwa – Kwamared Galadanchi

Published

on

Shugaban ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Right Network dake nan Kano Kwamared Umar Sani Galadanchi, ya ce tallafawa masu ƙaramin ƙarfi gida hanya da na Asibiti yakan tallafa musu wajen rage musu wani raɗaɗin rayuwa da yake damunsu.

Kwamared Umar Galadanchi ya bayyana hakan ne a yayin da tawagar su ta sauke kayan shan ruwa ga marasa lafiya a wasu ɓangare na Asibitin Murtala dake nan Kano a ranar Lahadi.

Yana mai cewa, sun kaiwa marasa lafiyar kayan shan ruwan ne domin rage musu wata damuwa da take damunsu na yau da kullum.

“Yana daga cikin wajibcin aikace-aikacen ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam su tallafawa masu ƙaramin ƙarfi da lafiya, karfi da kuma aljihu domin ragewa mutane wata damuwa da take damun su”. Inji Umar Galadanchi.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Umar Sani Galadanchi, ya kuma yi kira ga masu zuciya da su ƙara taimakawa al’umma musamman ma a wannan lokaci na Azumin watan Ramadan da ake ciki, da ake matuƙar buƙatar Mai-makon kashe dukiyoyin ta hanyar da basu da ce ba.

Continue Reading

Trending