Connect with us

Wasanni

Ina jajanta wa Mane a kan rashin halartar Qatar – Van Dijk

Published

on

Dan wasan baya na Netherlands, Virgil van Dijk, ya aike da sako ga dan wasan gaban Senegal, Sadio Mane, bayan an cire dan wasan Bayern Munich daga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022 a Qatar.

Van Dijk ya ce, Mane ya na daya daga cikin fitattun ‘yan wasa a duniya, kuma gasar cin kofin duniya za ta yi kewar dan wasan da yake da ingancinsa.

A cewarsa, yana jin zafin Mane, inda ya kara da cewa ya ji takaicin yadda ba zai iya buga wasa da abokinsa ba a gasar cin kofin duniya.

Dukansu Van Dijk da Mane sun kasance tsoffin abokan wasansu a Liverpool.

A ranar Litinin ne Netherlands za ta kara da Senegal a rukunin A kuma Mane ba zai buga ba saboda rauni.

“Ina jin tsoro gare shi (Sadio Mane) ya rasa gasar cin kofin duniya. Gasar ta cancanci mafi kyawun ‘yan wasa a duniya, kuma tabbas yana ɗaya daga cikinsu, “Van Dijk ya shaida wa ESPN.

“Har ila yau, abokina ne sosai, don haka na ji takaicin yadda ba zan iya buga wasa da shi ba.”

Ya kara da cewa, “Senegal tana da isassun ‘yan wasan da za su iya maye gurbinsa, amma ba kamarsa ba ne. Mane yana cikin wani nau’i na daban.”

Labarai

Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Published

on

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.

A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Continue Reading

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Trending