Wasanni
Da Duminsa: Qatar ta kwashi kashin ta a hannun Equador a wasan farko

Qatar mai masaukin baki ta bude gasar cin kofin duniya ta Fifa a shekarar 2022 cikin wasa mara dadi, a hannun Ecuador bayan ta doke su a wasan da suka fafata a filin wasa na Al Bayt da ci 2-0.
‘Yan wasan karkashin Felix Sanche, sun kasance tare a sansanin tsawon watanni shida da suka gabata, domin shirya gasar da kuma aiki da dabaru, amma rawar da ta taka da rashin jituwa ta kai ga rashin nasara a rukunin A.
Yayin da Senegal mai rike da kofin Nahiyar Afrika da kuma Netherlands za su fafata da wasan Qatar a wasan gaba.
An bude gasar mai ban mamaki, an ga bugun daga kai sai mai tsaron gida na Enner Valencia wanda ya zura kwallaye biyu a ragar Qatar

Wasanni
Kungiyar Al-Ittihad ta sallami mai horaswar ta Nuno.

Kungiyar kwallon kafa ta Al-Ittihad da ke kasar Saudiyyah ta sallami mai horaswar ta Nuno Espirito Santo, bayan kwashe watanni 16 ya na horas da ita.
Santo dan asalin kasan Portugal mai shekaru 49, kuma tsohon mai horas da Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta kasar Ingila, ya fara horas da kungiyar Al-Ittihad ne a watan Yuli na shekarar 2022 bayan korar sa da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta yi.
Kungiyar kwallon kafa ta Al-Ittihad dai ta bayyana cewar ta sallami Nuno Espirito Santo ne sakamakon rashin kokari da kungiyar ta ke yi karkashin jagorancin sa, Al-Ittihad dai tayi nasara ne a wasanni 6 cikin wasanni 12 da ta buga a kakar bana.
A ranar Litinin din da ta gabata ne, Kungiyar kwallon kafa ta Air Force ta kasar Iraq, ta doke Al-Ittihad da ci 2 – 0 a wasan zakarun Asian Champions league.

Wasanni
Kano Pillars ta koma mataki na hudu a gasar NPFL.

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta koma mataki na hudu a gasar cin kofin kwararru na Nigerian
Pillar dai ta doke Kungiyar kwallon kafa ta Bayelsa United ne, da ci uku babu ko daya a wasan mako na shida na gasar ta shekarar 2023 zuwa 2024.
A ranar lahadi 5/11/2023 ne kungiyar ta Kano Pillars za ta ziyarci Kungiyar kwallon kafa ta Sporting Lagos a Jihar Lagos a wasan mako na bakwai na gasar.

Wasanni
Sakamakon wasan mako na hudu na gasar NPFL

Sakamakon wasan mako na hudu na gasar cin kofin kwararru na Najeriya na kakar 2023/2024 wato NPFL.
Tun a ranar Asabar din da ta gaba ta ne 21 Oktoba 2023, aka buga wasa daya tilo kamar haka÷
Niger Tornadoes 1 – 0 Bayelsa United
Sai dai an dage wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Doma United da Enyimba
Wasanni da aka buga a ranar Lahadi 22 Oktoba 2023 kuwa÷
Gombe United 1 – 0 Bendel Insurance
Akwa United 0 – 0 Shooting Stars
Heartland Owerri 1 – 1 Katsina United
Kano Pillars 1 – 0 Rivers United
Kwara United 1 – 1 Enugu Rangers
Lobi Stars 2 – 0 Abia Warriors
Plateau United 1 – 0 Sunshine Stars
Remo Stars 2 – 1 Sporting Lagos.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano