Connect with us

Lafiya

Rahoto: Kada matashi ya bari a ba shi kudi ya sha kayan maye a lokacin zabe – Kwamared Mai Salati

Published

on

Wani matashi dan gwagwarmaya a jihar Kano, Kwamared Adamu Mai Salati Hausawa, ya ce, kada matashi ya bari a ba shi kudi ya sha kayan maye a lokacin zabe.

Kwamared Mai Salati, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Labarai

Cutar mashako ta bulla a wasu sassan Jigawa

Published

on

Akalla mutum goma ne suka mutu bayan ɓarkewar cutar mashaƙo a kananan hukumomi 14 na jihar Jigawa.

 

Ma’aikatar Lafiyar jihar ce ta sanar wa manema labarai haka a Dutse, a yau Lahadi. Ta ce ana kuma zargin cewa mutum 91 sun kamu da cutar.

 

Babban sakatare a ma’aikatar, Dr Salisu, Mu’azu, ya ce zuwa yanzu, an tabbatar da mutum biyu da suka kamu da cutar a kananan hukumomin Kazaure da Jahun yayin da aka Ɗauki jinin wasu zuwa Abuja domin yin gwaji da tantancewa.

 

Mu’azu ya ce ɓarkewar cutar abin damuwa ne musamman ma ganin cewa ta ɓulla a yankunan da ba su taɓa yin riga-kafin ta ba.

 

A cewarsa, tuni ma’aikatar ta fara bincike domin tattaro bayanai daga yankunan da abin ya shafa.

 

Ya ce gwamnatin jihar tuni ta fara shiri don yin riga-kafi a yankunan domin kaucewa yaɗuwar cutar.

Continue Reading

Lafiya

Gwamnatin Kano ta tabbatar da bullar cutar Mashako a jihar

Published

on

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta tabbatar da barkewar annobar cutar Tarin Mashako da cutar Lassa a kananan hukumomin jihar 13 da suka hadar da karamar hukumar Birni da Gwale da Fagge da Dala da Kumbotso Ungoggo da Nasarawa da Bichi da Rano Dawakin Tofa da Dawakin Kudu da Gwarzo Wanda Kuma a ranar 20 watan Janairu mutane 100 cikin mutane 8 da aka tabbatar sun kamu uku sun mutu yayinda 41 suka sami lafiya kawo yanzu dai sama da mutane 30 sun mutu saboda annobar.

Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Aminu Ibraham Tsanyawa ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya gudana da yammacin ranar Asabar.

Kwamishinan ya ce an fara samun cutar Lassa ne a asibitin Muhammadu Abdullahi Wase Wanda sakamakon gwaji ne ya tabbatar da hakan Wanda ke dauke da cutar ya dawo daga jihar Taraba inda yake kasuwanci Kuma daga baya ‘yan uwansa uku suma duk sun kamu.

An dai Samar da cibiyoyi a asibin Murtala Wanda Dr Salma Suwait ke jagoranci sai Kuma Fatima dake jagorantar cibiyar da ke asibitin koyarwa na Aminu Kano.

Kazalika cibiyar dake garin ‘Yar Gaya itama an Kara samar da likitoci duk da kawo yanzun babu mai dauke da cutar a kwance.

Daga cikin alamomi da ake gane cutar ta tarin Mashako akwai zazzabi Mai zafi da Tari kunbirin wuya sharkewar numfashi da futar jini daga gabobi cutar na Kuma taba zuciya da Koda.

Dakta Aminu Ibraham Tsanyawa ya ce daga cikin hanyoyin kariya akwai tsaftar muhalli da Sanya takunkumi da Kuma neman shawarar jami’an lafiya.

Continue Reading

Kimiya

SIKILA – Ko ka San matsalolin Ƙwayar Jini Mai Sikila?

Published

on

Shafin Physiotherapy Hausa ya bayyana cewa Ciwon sikila ko kuma amosanin jini, wato ‘Sickle Cell Disease’ a turance, ciwon jar ƙwayar halittar jini ne da ake gadar sa daga iyaye (mace da namiji). Lafiyayyiyar jar ƙwayar jini tana da sifar da’ira ne. Amma masu ciwon sikila, jar ƙwayar jininsu tana zama sifar lauje ko baka ne, wato ‘sickle’ a turance.

A yayin da mafi yawan sifar jar ƙwayar jini ta zama sifar lauje a ciki jini:

1] Wannan zai rage wa jar ƙwayar jinin ikon shaƙar wadatacciyar iskar oksijin daga huhu domin kaiwa zuwa sassan jiki.

2] Saurin tafiyar ƙwayar jinin a cikin jijiyoyin jini zai ragu.

3] Harɗewa ko sarƙewar jajayen ƙwayoyin jini yayin da suke gogayya a ƙoƙarin shiga siraran jijiyoyin jini.

4] Fashewa ko mutuwar ƙwayoyin jini kafin cikar wa’adin kwanaki 115 zuwa 120 da ya kamata su yi suna aiki a jiki.

Daga cikin matsalolin da masu ciwon sikila ke fuskanta akwai:

1. ƙamfar jini, wato ƙarancin jini a jiki, sakamakon yawan fashewar ƙwayoyin jinin kafin cikar wa’adinsu.

2. Kumburin fuska, tafukan hannu da sawu.

3. Jinkirin girman jiki da tsaikon balaga.

2. Matsanancin ciwon jiki da gaɓɓai.

4. Sauri ko yawan harbuwa da ƙwayoyin cutuka da ke kama ƙashi da gaɓoɓi.

5. Lalacewar ƙashi da ruɓewar sassan jiki da dai sauransu.

Likitocin fisiyo na ba da gudunmowa ga masu ciwon sikila yayin da suka gamu da matsalolin da ke tattare da ciwon sikila kamar: matsanancin ciwon jiki da gaɓoɓi, riƙewar gaɓoɓi, raunin ko rashin ƙwarin tsokokin jiki, dashen gaɓar ƙugu, dashen gaɓar gwiwa, yanke sassan jiki, jinkirin matakan girman yaro da dai sauransu.

Muradin likitan fisiyo ga mai ciwon sikila shi ne samun rayuwa cike da aiki cikin kuzari da karsashi ba tare da ciwo ko nakasa ba.

MATAKIN KARIYA

Daga ƙarshe, ana iya kauce wa haɗarin haifar yaro mai ciwon sikila ta hanyar yin gwajin ‘genotype’ ga ma’aurata kafin aure domin gano yiwuwa ko akasin haifar yaro mai sikila.

Tabbata ka san gwajin ‘genotype’ ɗinka da na wace za ka aura domin tabbatar da cewa ba ku da haɗarin haifar yaro mai ciwon sikila.

Continue Reading

Trending