Connect with us

Labarai

Mahukunta ku kara kaimi na tallafawa mara karfi – Dagacin Bachirawa

Published

on

Dagacin garin Bachirawa Kwanar Madugu Alhaji Haruna Bello, ya ja hankalin mahukunta da su ƙara tallafawa masu ƙaramin ƙarfi, domin rage musu wani raɗaɗi da ke damun su na yau da kullum.

Dagacin ya bayyana hakan ne ta bakin wakilinsa Mallam Muhammad Haruna Bello, yayin duba lafiyar mazauna yankin maza da mata tare da basu magunguna kyauta, wanda kwamitin masallacin juma’a na Madinatul Qur’an dake unguwar Bachirawa ƙarƙashin jagorancin Alƙali Umar Sunusi Ɗan Baba, wanda ya gudana a ƙarshen makon nan, muna tafe da rahoto a labaran mu na gaba.

Dagacin ya bayyana hakan ne ta bakin wakilinsa, Mallam Muhammad Haruna Bello, yayin duba lafiyar al’ummar yankin na Bachirawa tare da basu magunguna kyauta, wanda kwamitin masallacin juma’a na Madinatul Qur’an dake unguwar ƙarƙashin jagorancin Alƙali Umar Sunusi Ɗan Baba, wanda ya gudana a ƙarshen makon nan.

Wasu daga cikin mutanen da aka duba gami da basu magungunan kyauta, sun ce duba lafiyar tasu an yi ne a kan gaɓa.

Alƙali Umar Sunusi Ɗan Baba, ya ce, Kwamitin masallacin na Madinatul Qur’an, ya yi haɗin gwiwa ne da wani dan kasuwa, domin tallafawa al’ummar yankin musamman ma marasa lafiya.

Jagoran likitocin da aka tanadar don su duba marasa lafiyar kyauta, mai suna Dr. Musa Abdullahi Ishaq, ya ce duba lafiyar mutanen yankin ya shafi kwanaki biyu wato Asabar da Lahadin ƙarshen makon da mu ka yi bankwana da shi.

Baba Suda

NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Published

on

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.

 

Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.

 

A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.

Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

Continue Reading

Labarai

Real Madrid ta kaddamar da Alexander

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta ƙaddamar da ɗan wasa Trent Alexander Arnold a yau a matsayin ɗan wasan ta

Inda shugaban ƙungiyar Flerontino Perez yace yau suna matuƙar Farin ciki kasancewar sun mallaki babban ɗan wasan baya a duniya.

 

Shima ɗan Wasa Arnold ya bayyana cewa yana cikin farin ciki kuma mafarkin sa ya cika na zama ɗan Wasan Madrid a yau.

Continue Reading

Daurin Boye

Zan shiga kawancen ‘yan jamiyyar hamayya – tsohon Minista

Published

on

Tsohon ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce a shirye yake don shiga ƙawancen ƴan jamiyyar hamayya domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027

A wata hira da BBC, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce suna ƙoƙarin samar da haɗakar siyasar da za ta samar da sauyi a ƙasar.

Amaechi wanda ɗan jam’iyyar APC ne  ya nuna damuwa kan abin da ya ƙira halin ƙuncin rayuwa da ƙasar ke ciki.

Amaechi ya ce bai cire tsammanin yin takarar shugaban ƙasa ba, illa lokaci ne kawai zai tantance.

Continue Reading

Trending