Connect with us

Manyan Labarai

Da Muninsa: Manchester United ta yanke hulda da Ronaldo

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sallami dan wasan Portugal, Cristiano Ronaldo, nan take.

Matakin dai ya biyo bayan wata tattaunawa mai cike da cece-kuce da dan wasan mai shekaru 37 ya soki kungiyar kuma ya ce, ba ya mutunta kocin kungiyar Erik ten Hag.

Bangarorin biyu sun bayyana cewa sallamar ta Ronaldo “an amince da juna nan take”.

Sanarwar da Manchester United ta fitar ta ce “Kungiyar ta gode masa saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar tsawon shekaru biyu a Old Trafford.”

Sun yi fatan alheri ga “shi da iyalinsa a nan gaba” kuma sun kara da cewa “kowa a Manchester United ya ci gaba da mai da hankali kan ci gaba da kai kungiyar a karkashin Erik ten Hag da kuma yin aiki tare, domin samar da nasara a filin wasa”.

Ronaldo ya na tare da Portugal a gasar cin kofin duniya da ake yi a Qatar kuma ya na shirin jagorantar su a wasan farko na rukunin H da Ghana ranar Alhamis.

“Bayan tattaunawa da Manchester United mun amince tare da kawo karshen kwantiragin mu da wuri,” in ji wata sanarwa daga dan wasan.

“Ina son Manchester United kuma ina son magoya baya, hakan ba zai taba canzawa ba. Duk da haka, ya  na jin lokacin da ya dace da ni domin neman sabon kalubale.

“Ina yiwa kungiyar fatan samun nasara a sauran kakar wasanni da kuma nan gaba.”

Labarai

Rahoto: Kada a kwanta bacci da wuta lokacin sanyi – Hukumar kashe gobara

Published

on

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta ce, akwai hadari kwanciya da wuta, domin dumama daki a lokacin sanyi.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara a jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin kudi ya janyo sana’ar Gwanjo ta ja baya – Mai sana’ar Gwanjo

Published

on

Wani sana’ar sayar da Gwanjo a kasuwar kofar Wambai, Adamu Kala ya ce, sana’ar gwamjo ta ja baya a wannan shekarar, saboda tsada da kuma rashin kudi

Adamu Kala, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il, yana mai cewar, idan aka kwatanta da baya, an samu ja bayan sana’ar.

Akwai cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Duk maganin da za a sha babu umarnin likita haramtacciyar kwaya ce – PSN

Published

on

Kungiyar masu hada magani Pharmacertical Society of Nigeria PSN reshen jihar Kano, ta ce, amfani da miyagun kwayoyi babbar hanyar rusa tattalin arziki da lafiya dama rasa rayuwa gaba daya ne.

Shugaban kungiyar masu hada magani Pharmacertical Society of Nigeria PSN reshen jIhar Kano ne, Sani Ali Yusuf ya bayyana hakan, yayin wani taro da kungiyar da hadin gwiwar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA suka shirya.

Ya ce, duk wani magani da mutum zai dinga amfani da shi ba tare da umarnin likita ba to ya zama haramtacciyar kwaya kuma tana da illa.

Ana sa bangaren, kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a jihar Kano Alhaji Abubakar Ahmad Idris, ya bayyana cewar, babu wani mashahurin mutum mai yin amfani miyagun kwayoyi.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il, ya rawaito cewar, an shirya taron ne da nufin wayar da kan al umma, dangane da illolin yin ta’ammali da miyagin kwayoyi.

Continue Reading

Trending