Connect with us

Wasanni

Kwaikwayon murnar Ronaldo da na yi ba ya na nufin na raina shi ba ne – Dan Wasan Ghana

Published

on

Dan wasan gaba na Ghana Osman Bukari ya ce, bai raina Cristiano Ronaldo ba a lokacin da ya kwaikwayi murnar kwallon da tauraron dan kwallon Portugal ya zura a raga.

Bukari ya zura kwallo a raga inda aka tashi 3-2 a minti na 89 daga bisani ya murna irin ta fitaccen hoton Ronaldo na ‘Siu’.

Tsohon dan wasan na Manchester United ya baiwa Portugal damar ci gaba da cin kwallo a filin wasa na 974 da ke Doha amma sai da Bukari ya farke daga yadi shida.

“Na lura murna ta ta haifar da maganganun da ke cewa na raina Ronaldo,” dan wasan mai shekaru 23 ya wallafa a shafin Twitter.

“Wannan ba daidai ba ne, na ji dadin lokacin da na ci wa kasata kwallo a gasar cin kofin duniya da na yi a karon farko da ya kai ni ga murna.

Labarai

Real Madrid ta kaddamar da Alexander

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta ƙaddamar da ɗan wasa Trent Alexander Arnold a yau a matsayin ɗan wasan ta

Inda shugaban ƙungiyar Flerontino Perez yace yau suna matuƙar Farin ciki kasancewar sun mallaki babban ɗan wasan baya a duniya.

 

Shima ɗan Wasa Arnold ya bayyana cewa yana cikin farin ciki kuma mafarkin sa ya cika na zama ɗan Wasan Madrid a yau.

Continue Reading

Labarai

Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Published

on

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.

A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Continue Reading

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Trending