Connect with us

Wasanni

UEFA ta bude bincike a kan Juventus bayan laifin da ake tuhumar kungiyar

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, Uefa ta bude bincike a kan Juventus kan yuwuwar keta ka’idojin bayar da lasisin kungiyar da kuma ka’idojin wasa na kudi.

A watan Agusta, Uefa ta cimma matsaya da Juventus bisa bayanan kudi tsakanin shekarar 2018 zuwa 2022, kuma a ranar litinin hukummomin kungiyar suka yi murabus saboda matsalar kudi.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton a ranar Alhamis cewa, masu shigar da kara na Italiya sun bukaci tsohon shugaban Juve Andrea Agnelli da wasu mutane 11 da kuma kungiyar da kanta su gurfana a gaban kuliya bisa zarge-zargen lissafin karya.

Masu gabatar da kara a Turin, inda Juve suke, sun gudanar da bincike a kan lissafin kungiyar da kuma bayanan da aka yi wa kasuwannin hada-hadar kudi a cikin shekaru uku da suka gabata.

Suna zargin kungiyar ta gaza bayyana asarar kudaden da ta yi a kakar wasanni uku a kakar 2018-19, 2019-20 da 2020-21.

Sun yi la’akari da kimar da aka danganta ga musayar ‘yan wasa tsakanin kungiyoyi, kamar yadda aka bayyana, an sadaukar da albashi yayin annobar Covid-19 ko kuma an jinkirta shi kawai.

Hukumar La Liga ta Spain ta fitar da wata sanarwa a ranar Talata, inda ta sake sabunta kiran da ta yi na a sanya mata “takunkumin wasanni na gaggawa” a kan Juve, wacce ta kare a mataki na hudu a gasar bara, kuma ta yi asarar Yuro miliyan 254.3 (£220m) – wani tarihi a Italiya.

A watan Nuwamban da ya gabata, Juventus ta ce, ta na ba ‘yan sanda hadin kai bayan da aka fara gudanar da bincike kan cinikin kungiyar.

Hukumar kula da harkokin kudi ta Uefa (CFCB) ta fara sasantawa ne bisa bayanan da Juve ta gabatar dangane da shekarun kudaden da suka kare a 2018, 2019, 2020, 2021 da 2022.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending