Connect with us

Wasanni

Hukumar kwallon kafa ta Afrika ta taya Senegal murna duk da an yi waje da ita

Published

on

Hukumar kula da kwallon kafa ta Afrika CAF, ta yaba wa kungiyar Terangha Lions ta Senegal, duk da fitar da kasar daga gasar cin kofin duniya ta FIFA na 2022 a Qatar.

Tawagar Aliou Cisse ta yi rashin nasara da ci 3-0 a hannun ‘yan wasan zakuna Uku na Ingila a wasan zagaye na 16 da suka fafata a daren Lahadi.

Zakarun na Afirka sun fara wasan da kyau, amma daga baya sun yi rashin nasara inda Ingila ta samu ta hannun Jordan Henderson da Harry Kane da kuma Bukayo Saka.

CAF ta yabawa kungiyar ta Terangha Lions bisa yadda nahiyar ke alfahari da gasar.

“Kasashen Afirka sun sanya mu duka abin alfahari. Tafiya ta #FIFAWorldCup ta Senegal ta zo karshe, amma tabbas za mu sake ganin su a 2026, “CAF ta rubuta a shafinta na internet.

Kungiyar kwallon kafa ta Atlas Lions ta Morocco za ta fafata da Spain a wasan zagaye na 16 a ranar Talata.

Wasanni

Tsohon mai horas da Super Falcons Mabo ya rasu.

Published

on

Tsohon mai horas da tawagar ‘yan wasan kwallon kafa ta mata ta kasa, Super Falcons, Ismaila Mabo, ya rasu ya na da shekaru 80 a duniya.

Dan uwansa Salisu Nakande Mamuwa ne ya bayyana rasuwar ta sa a shafin sa na sada zumunta a safiyar yau Litinin.

Karanta wannan labarin: http://flying eagles

Kafin rasuwarsa dai Ismaila Mabo ya jagoranci Super Falcons a gasar cin kofin duniya na mata, inda ya jagorance su zuwa wasan dab da na kusa da na karshe a shekarar 1999, ya kuma jagorance su zuwa gasar wasannin Olympics a shekarar 2000 da kuma 2004.

Continue Reading

Wasanni

Silva ya tsawaita kwantaraginsa da Chelsea

Published

on

Thiago Silva wanda ke buga wasa a baya, ya sake tsawaita kwantaraginsa da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na tsawon shekara daya, inda kwantaragin zai kare a shekarar 2024.

Silva mai shekaru 38, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Chelsea daga PSG ta kasar Faransa a shekarar 2020, kawo yanzu ya bugawa Chelsea wasanni 106.

Thiago Silva wanda dan asalin kasar Brazil ne, ya tallafawa Chelsea ta samu nasarori da dama wanda daga ciki harda nasarar lashe kofin zakarun nahiyar Turai.

Continue Reading

Wasanni

Za a iya Conte aikin gaggawa a mafutsara – Tottenham

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur, ta baiwa mai horas da kungiyar, Antonio Conte, hutu yayin da a yau ake shirin yi masa aikin tiyatar gaggawa a mafutsararsa.

Kungiyar ta Tottenham ta tabbatar da hakan a wata sanarwar da ta wallafa a shafin ta na internet.

Conte ya kamu da rashin lafiya a farkon wannan makon, kuma ya koka da matsanancin ciwon ciki.

An gano tsohon manajan na Chelsea ya na da cutar cholecystitis, yanayin da ke haifar da kumburi da ja na mafutsara.

Labarai mai alaka: Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta dauki aron Danjuma daga Villarreal

Sanarwar ta Tottenham ta ce “A kwanan nan Antonio Conte ya yi rashin lafiya tare da matsanancin ciwon ciki.”

“Bayan an gano cutar cholecystitis, yau za a yi masa tiyata a mafitsara a yau, kuma zai dawo bayan wani lokaci idan ya samu murmurewa. Kowa a kungiyar ya na yi masa fatan alheri.” Inji Tottenham.

Continue Reading

Trending