Labarai
Rahoto: Rashin kudi ya janyo sana’ar Gwanjo ta ja baya – Mai sana’ar Gwanjo

Wani sana’ar sayar da Gwanjo a kasuwar kofar Wambai, Adamu Kala ya ce, sana’ar gwamjo ta ja baya a wannan shekarar, saboda tsada da kuma rashin kudi
Adamu Kala, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il, yana mai cewar, idan aka kwatanta da baya, an samu ja bayan sana’ar.
Akwai cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Kannywood
Hukumar tace finafinai ta dage dakatarwar da ta yiwa wasu finafinai

Hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta amince da tsawaita wa’adin dakatar da nuna wasu manyan fina-finai masu dogon zango 22.
Tun da farko hukumar ta sanar da dakatar da nuna finafinan ne sakamakon zarginsu da saɓa ƙa’idar hukumar, sannan ta ba masu finafinan mako ɗaya su cika ƙa’idojin hukumar.
Sai dai a wata sanarwa da shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Najeriya (MOPPAN) reshen jihar Kano, Ado Ahmad Gidan Dabino, ya ce an tattauna, kuma an fara samun masalaha.
“Bayan doguwar tattaunawa da shugaban hukumar, Abba Al-Mustapha da wasu ma’aikatansa da wakilan Kannywood, an samu matsaya a kan:
Hukumar ta yarda ta ƙara mako ɗaya a cigaba da sakin finafinan da suke a layin fitowa don kada masu finafinan su yi asara
Za a sake zama ranar Alhamis domin sake tattaunawa domin a ƙarƙare maganar.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai wakilan MOPPAN da Abdul Amart da Nazifi Asnanic da Abubakar Bashir Maishadda da sauransu.

Baba Suda
Dumamar yanayi :- Gwamna Zulum ya haramta sare bishiyu

Gwamnan jihar Borno Baba Gana Umar Zulum ya kaddamar da wasu dokokin biyu ga al’ummar Jihar.
Dokar farko itace Gwamnan ya haramta sare bishiyu a dukkanin fadin jihar, Inda kuma ya Kara kaddamar da dokar tsaftace muhalli a dukkanin karshen wata.
Yayin da yake kaddamar da dokar Gwamna Zulum yace duba da dumamar yanayi da ake fuskanta a yanzu gwamnati ta haramta sare bishiyu a fadin jihar Borno.
Haka kuma saboda Kare lafiya da kuma al’ummar Jihar dole ne dukkanin karshen wata a gudanar da tsaftar muhalli a Jihar Borno.
” A matsayi na Wanda kundin tsarin mulkin kasa ya bani dama, ni Baba Gana Umara Zulum na haramta sare bishiyu a fadin jihar Borno, kuma na saka dokar wajibi ne kowa ne dan Jihar ya tsaftace muhalli a dukkanin karshen wata, saboda inganta lafiyar al’ummar Jihar Borno.”

Labarai
Ƙauracewa masu unguwanni wajen bada hayar gida ko sayarwa na kawo matsalar Tsaro a Kano – Mai Unguwa

Mai unguwar Chiranchi unguwar Kwari B, bayan Sani Abacha Youth Center da ke jihar Kano, Hafizu Garba Saminu, ya ce sanar da masu unguwanni harkokin saye da sayarwar Ƙasa da gidaje, da kuma sanya ido a cikin unguwanni don kare kai, na daga cikin hanyoyin daƙile matsalar Tsaro a sassan jihar.
Mallam Hafizu Garba, ya bayyana hakan ne a zantawar sa da tashar Dala FM Kano, ya kuma ce akwai buƙatar Dillalai su ci gaba da basu haɗin kan da ya dace tare da bin tsari a harkar su, don daƙile matsalar tsaron.
“A mafi yawan lokuta idan aka samu matsalar tsaro a cikin unguwanni akan ɗora laifin ga masu unguwanni, bayan kuma ba kasafai ake sanya su a cikin bayar da hayar gida ko sayar da Filaye ba, ballantana su san waɗanda za a sayarwa ko bai wa Hayar wanda hakan ke ƙara kawo matsalar tsaron, “in ji shi”
Mai unguwar ya kuma ce indai za a rinƙa sanya masu unguwanni cikin lamuran tsaro, ta haka ne za a daƙile matsalar tsaron, kasancewar su ne mafi kusanci da al’umma, inda ya kuma yi kira ga jama’a da su bada dukkan gudunmawar su don ganin an daƙile matsalar tsaro a sassan jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su