Wasanni
Ina goyon bayan ka duk da ka yi kuka sosai na kishi – ‘Yar uwar Ronaldo
‘Yar’uwar Cristiano Ronaldo, Elma Aveiro, ta mayar da martani ga faifan bidiyo na dan uwanta yana kuka bayan fitar da Portugal daga gasar cin kofin duniya ta FIFA a Qatar na 2022.
Ronaldo ya dai fashe da kuka, bayan da Morocco ta fitar da Portugal daga gasar cin kofin duniya a karshen mako.
An ga tsohon dan wasan na Manchester United ya na kuka a lokacin da ya fice daga cikin fili a karshe na wasan.
Dan wasan mai shekaru 37, ya shigo ne daga kan benci yayin da Morocco ta doke Portugal da ci 1-0 a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya bayan Youssef En-Nesyri ya ci kwallo daya tilo a wasan.
Daga nan sai Ronaldo ya bar filin wasa yana kuka a lokacin da Morocco ta fitar da su daga gasar cin kofin duniya ta 2022.
Da take mayar da martani, Aveiro, a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram a ranar Litinin, ta ce, faifan bidiyon Ronaldo na kuka ya na da kyau kuma ba za ta gaji da kallonsa ba.
“Kyakkyawan hoto, soyayya, godiya, kima, dabi’u ne da ba kowa ke da shi ba… Ya na da kyau wannan bidiyon da ba na gajiya da kallo, kuma ba Portuguese ba ne, ban sani ba ko na sanya kaina fahimtar girman kai, babban mutum kasancewarsa, babban ɗa, ɗan’uwa, uba, abin koyi ga kowa da kowa.
“Na gode wa Allah da ya ba ni a matsayina na ɗan’uwa kuma mutumin da na ke alfahari da shi da ƙauna da dukkan ƙarfina. Godiya ga Allah. Na gode, Ronaldo, ” Ta wallafa tare da bidiyon.
Wasanni
Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.
Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.
Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.
Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.
Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.
Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.
Wasanni
Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba
Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.
Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.
Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.
Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.
Wasanni
Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.
Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.
Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.
A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.
Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su