Connect with us

Labarai

Kotu ta yanke wa wata matashiya hukuncin kisa ta hanyar rataya a Kano

Published

on

Babbar kotun jiha mai lamba 9, karkashin jagorancin Justice Amina Adamu Aliyu ta yanke hukuncin kisa ta hanya rataya akan wata matashiya mai suna Aisha Kabiru Danbare.

Tun da farko gwamnatin jiha ce ta gurfanar da Aisha a gaban kotun bisa tuhumar kisan kai.

Kunshin zargin da ake yiwa Aisha ya bayya cewar, a ranar 12 ga watan 12 na shekarar bara Aisha Kabiru ta yi amfani da wuka ta hallaka wata makociyar su mai suna Bahijja Abubakar ta hanyar soka mata wukar a wuya, sakamakon rashin fahimtar da suka samu.

Lauyan gwamnati Lamido Abba Soron Dinki, ya gabatar da shaidu 3 yayin da Aisha ta kare kanta ita kadai.

Justic Amina Adamu ta ayyana cewar kotun ta gamsu babu kokonto akan tuhumar da ake yiwa Aisha, saboda haka kotun ta bayyana cewa, ta zartas da hukuncin kisa ta hanyar rataya akan ta.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaita cewa, laifin ya saba da sashi na 221 na kundin Penal Code.

Hangen Dala

Zargin Almundahana:- An kama jami’in gwamnatin Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama Tasiu Al’amin-Roba, babban mataimaki na musamman (SSA), ga gwamnan jihar kano da kuma wani Abdulkadir Muhammad bisa zargin su da karkatar da kayan abincin tallafi a jihar Kano.

 

Kwamishinan ‘yan sandan, Hussaini Gumel, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN hakan a wata hira ta wayar tarho a ranar Lahadi cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani dakin ajiyar kaya da ke Sharada dauke da jakunkuna sama da 200.

 

Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun yi awon gaba da shinkafa da masara a ma’ajiyar da ke Sharada.

 

“Tun daga lokacin ne muka fara bincike mai zurfi don gano buhunan masara ko shinkafa nawa aka diba aka sayar da su,” inji shi.

 

Gumel ya ce za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu bayan kammala bincike .

Continue Reading

Hangen Dala

An yiwa kasafin Kudin 2024 karatu na biyu

Published

on

Majalisar Dattawan Najeriya da ta Wakilai sun yi wa kasafin kuɗin ƙasar na 2024 karatu na biyu ranar Juma’a kwana biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya gabatar musu da shi.

A ranar Laraba ne Tinubu ya je majalisar tare da gabatar da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin abin da gwamnatinsa za ta kashe a 2024, kuma ya nemi ‘yan majalisar su gaggauta amincewa da shi.

Sai dai shugaban bai bayyana adadin abin da kowace ma’aikata da hukumomin gwamnati za su samu ba a lokacin da ya yi gabatarwar, abin da ya jawo cecekuce da muhawara a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito ‘yan majalisar na kokawa yayin muhawarar da suka yi ranar Juma’a game da ƙarancin bayanai kan kasafin, wanda suka ce ya sa sun mayar da hankali ne kawai kan abubuwan da Tinubu ya faɗa a jawabinsa.

Jam’iyyun adawa sun soki kasafin da cewa “na yaudara ne”, yayin da Shugaba Tinubu ya yi masa laƙabi da “kasafin sabunta fata”.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Kano za ta Kara inganta aikin Jarida

Published

on

Gwamnatin jihar kano tace za ta hada Kai da kungiyar ‘yan jarida masu magana a Radio da Television na kasa wato Society of Nigerian Broadcasters domin kara inganta aikin Jarida.

 

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Baba Halilu Dan Tiye ne ya tabbatar da hakan lokacin da ake kaddamar da ‘ya’yan kungiyar anan kano.

 

Baba Halilu yace duba da muhimmancin da aikin jarida ke dashi a tsakanin al’umma ya sanya gwamnatin Kano za ta cigaba da baiwa bangaren muhimmanci.

Taron Wanda ya gudana a cibiyar ‘yan Jaridu ta Kano ya samu halartar Mafi yawa daga cikin shugabannin kafafen yada labaran Dake Kano.

Continue Reading

Trending