Connect with us

Wasanni

Sergio Busquets ya yi ritaya daga buga kwallon kafa

Published

on

Dan wasan kasar Sipaniya, Sergio Busquets, ya sanar da yin ritaya daga buga kwallo a kasarsa ta Spaniya.

Dan wasan tsakiyar mai shekaru 34, wanda ya lashe gasar cin kofin duniya a shekara ta 2010 da kuma gasar cin kofin nahiyar Turai ta 2012, shi ne kyaftin din kasar da aka fitar a zagaye na 16 na karshe a bana a kasar Qatar.

“Bayan kusan shekaru 15 da wasanni 143, lokaci ya yi da za a yi bankwana da tawagar kasar,” kamar yadda ya rubuta a dandalinshi na sada zumunta.

“Abin alfahari ne na wakilci tawagar kasa ta da kuma taimaka wajen daukaka ta.”

Busquets shi ne na karshe daga cikin manyan ‘yan wasan tsakiya na Barcelona guda uku na Sipaniya tare da Andres Iniesta da Xavi wanda suka sanar da yin ritaya daga buga wasan kasa da kasa.

Ya buga wasansa na farko a Spain a ranar 1 ga Afrilu, 2009 a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya da Turkiyya, kuma ya ci gaba da taka leda a gasar cin kofin duniya hudu da na Turai uku.

Ya shafe tsawon rayuwarsa a wasa tare da Barcelona, wanda ya buga kusan sau 700, inda ya lashe kofuna da dama, ciki har da kofunan La Liga takwas da na gasar zakarun Turai sau uku.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending