Wasanni
FIFA za ta sake duba tsarin gasar cin kofin duniya na 2026 – Infantino
Fifa za ta sake duba tsarin gasar cin kofin duniya ta 2026 a Amurka, Mexico da Canada, in ji shugaban hukumar Gianni Infantino.
Kungiyoyin za su kara daga 32 zuwa 48 a gasar, kuma an tsara za a raba su zuwa rukuni 16 daga cikin uku, yayin da biyun da ke kan gaba za su wuce zuwa 32 na karshe.
Infantino ya ce, za a duba hakan ne bayan nasarar da kasashe hudu suka samu a gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar.
Infantino ya ce “A nan kungiyoyin hudu sun kasance abin ban mamaki.”
“Har minti na karshe na wasan karshe ba za ku san wanda zai lashe wasan ba.
“Dole ne mu sake duba ko kuma a sake tattauna tsarin. Wannan wani abu ne da tabbas zai kasance cikin manufar mu a taron na gaba.”
Gasar rukuni-rukuni da aka yi a Qatar sun hada da wasu wasannin karshe masu kayatarwa yayin da kasashen ke kokarin samun matsayi na biyu, domin samun tikitin zuwa zagaye na 16 na karshe.
An yi amfani da tsarin rukuni-rukuni na rukuni-rukuni hudu, tare da manyan biyun da suka tsallake zuwa zagaye na gaba, tun bayan da aka fadada gasar cin kofin duniya ta maza zuwa kasashe 32 a shekarar 1998.
Infantino ya ce “Na gode wa duk wanda ke da hannu a ciki, Qatar, da duk masu aikin sa kai don yin wannan gasar cin kofin duniya mafi kyau da aka taba yi.
Wasanni
Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.
Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.
Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.
Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.
Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.
Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.
Wasanni
Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba
Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.
Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.
Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.
Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.
Wasanni
Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.
Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.
Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.
A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.
Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su