Labarai
Keken da aka ƙi sayar wa Naira Miliyan 40 a Saudiyya

Mutumin nan ɗan asalin jihar Plateau, Aliyu Abdullahi Obobo, wanda ya je kasar Saudiyya akan Keke ya ce, an nemi ya sayar da Kekensa Naira Miliyan 40 a can ƙasar ya ƙi sayarwa.
Aliyu Abdullahi Abobo, ya bayyana hakan ne, a zantwarsa da gidan rediyon Dala a ranar Alhamis.
Ya ce, saboda yana buƙatar a karɓi Keken a ajiye shi a gidan tarihi na Najeriya, shi yasa ya ƙi sayar wa a can Saudiyya, kuma ko kyauta ne zai iya bayar wa a Najeriyar, domin ‘yan yara masu tasowa su amfana da tarihin.

Labarai
Zan haɗa kai da hukumomin tsaro da Baturan ƴan Sanda don magance matsalolin tsaro a Kano – CP Bakori

Sabon kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Dr. Ibrahim Adamu Bakori, ya ce zai haɗa kai da dukkannin hukumomin tsaro da baturan ƴan sandan da ke kan iyakokin jihar, don ganin an sami ingantacciyar tsaro a faɗin jihar.
Dr. Ibrahim Bakori ya bayyana hakan ne a zantawar sa da manema labarai ciki har da wakilin tashar Dala FM Kano, a ranar Laraba 19 ga watan Maris ɗin 2025.
Ya kuma ce zai amfani da fasahar sadarwa wajan gudanar da aikin sa, tare kuma da wayar da akan al’umna kasancenwar aikin tsaro na kowa ne.
A makon da ya gabata ne dai rundunar ƴan Sanda ta ƙasa ta turo CP Ibrahim Adamu Bakori, jihar Kano, wanda ya maye gurbin Salman Dogo Garba, bisa samun ƙarin girma da ya yi zuwa matakin AIG.

Labarai
Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ƙaryata ficewar sa daga APC zuwa SDP

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya musanta wata jita-jita da ake yaɗawa kan cewar ya fice daga cikin jam’iyyar APC mai mulki a ƙasa, zuwa SDP, al’amarin da ya ce bashi da tushe ballantana makama.
A cikin wata sanarwar da mashawarci na musamman ga tsohon Sanatan a kafafen yaɗa labarai Ezrel Tabiowo, ya fitar a jiya Lahadi, ta ce jita-jitar da ake yaɗawa na cewar Ahmad Lawan ya fice daga jam’iyyar ta APC, ƙarya ce tsagwaronta.
Jaridar Daily trust ta ruwaito cewar, sanarwar ta kuma ce, har yanzu Ahmad Lawan ɗan Jam’iyyar APC ne, kuma yana biyayya ga jam’iyyar, wadda yake alfahari da ita.

Labarai
Babu adalci a ƙarin kuɗin Data da na kiran Waya da aka yi a Najeriya – Human Rights

Ƙungiyar wayar da kan jama’a da kare haƙƙin ɗan adam da kuma tallafawa mabuƙata a Najeriya, ta ce Abin takaici ne yadda gwamnatin tarayya ta amince da ƙarin kuɗin Data da na kira, al’amarin da ta kira da rashin adalci ga ƴan Ƙasa.
Daraktan ƙungiyar ta Awareness for Human Rights and Charity Foundation a Najeriya Kwamared Auwal Usman Awareness, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya aikowa tashar Dala FM Kano, a ranar Lahadi.
“Ƙarin kuɗin Data da na kiran waya da kamfanonin sadarwa suka yi wa al’umma a Najeriya, abin damuwa ne, saboda ƙarin ya zo ne a dai-dai lokacin da jama’a ke fama da matsin tattalin arziƙi, da hauhawar Farashi, da wahalhalun Rayuwa, “in ji Auwal Usman”.
Ya kuma ce duba da halin mummunan tasirin wannan karin na kuɗin Data da na kiran Waya, kamata ya yi gwamnatin tarayya ta umarci kamfanonin sadarwar su sauƙaƙa wa al’umma saɓanin yi musu ƙarin.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ɗin, ta Awareness for Human rights and Charity Foundation, ta kuma buƙaci a soke ƙarin kuɗin kira da na datar da aka yi, tare da kafa dokoki da za su hana ƙara farashin ba tare da tuntuɓar al’umma ba.
Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, tuni dai ƴan Najeriya suka fara nuna takaicin su kan ƙarin kuɗin kira da na datar da kamfanonin sadarwa suka yi musu, lamarin da suke ci gaba da kira ga mahukunta da a rage kudaɗen bisa yadda ƙarin ya yi yawa.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su