Connect with us

Wasanni

Messi ne zai lashe kyautar Ballon d’Or maimakon Mbappe – Lewandowski

Published

on

Dan wasan gaba na Barcelona, Robert Lewandowski, ya bayyana kyaftin din Argentina, Lionel Messi, a matsayin dan wasan da ya kamata ya lashe kyautar Ballon d’Or ta 2023.

Messi ya kai matsayin gwarzon kwallon kafa a lokacin da ya lashe gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022 a Qatar a ranar 18 ga Disamba.

Dan wasan gaba na Paris Saint-Germain ya ci kwallaye biyu a daidai lokacin da Argentina ta doke Faransa a wasan karshe na gasar cin kofin duniya a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da suka tashi 3-3 bayan mintuna 120 a filin wasa na Lusail.

Lewandowski ya yi imanin saboda haka, Messi yanzu shi ne dan wasan da aka fi so ya lashe kyautar Ballon d’Or ta 2023, maimakon dan wasan Faransa Kylian Mbappe.

Da yake magana da Mundo Deportivo, dan kasar Poland ya ce, “Tabbas. Watakila akwai dan wasa guda daya [Mbappe] da ke taka leda a kulob daya, amma akwai gasar cin kofin duniya guda daya da za ta tantance wanda zai lashe ta [Ballon d’Or] a kakar wasa ta bana, kuma Leo [Messi] yanzu yana kan gaba, tabbas saboda abin da ya samu wanda ke nufin komai a gare shi.” in ji tsohon dan wasan Bayern Munich.

Labarai

Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Published

on

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.

A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Continue Reading

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Trending